FBI na Fargabar Sakin Bayanan Zargin Tinubu a Amurka Ya Jawo Babban Hadari
- FBI ta nemi izinin kotun Amurka da ta gabatar mata da wasu bayanai a ɓoye kan dalilin da ya sa ta ƙi sakin wasu bayanan bincikenta da suka shafi zargin Bola Tinubu
- Hukumar ta ce bayyana wasu daga cikin bayanan zai iya tona asirin dabarun binciken jami'an tsaro tare da jefa rayuwar wasu mutane cikin haɗari
- FBI ta ce ba za ta iya bayyana dukkan dalilan da suka sa ta riƙe wasu bayanai a bainar jama'a ba, saboda haka take neman gabatar da bayanan ga alkalin kotun shi kaɗai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI, ta shigar da ƙara a wata kotu tana neman izinin gabatar da bayanan sirri kan dalilin da ya sa ta ƙi sakin wasu bayanan bincike da suka shafi Shugaba Bola Tinubu.
FBI ta gabatar da bukatar ne a ranar 20 ga Agusta, 2026, inda ta nemi kotun ta ba ta damar gabatar da wata sanarwa ta musamman da za a duba a ɓoye.

Source: Facebook
The Cable ta ce hakan na nufin za a samu rubutacciyar sanarwa da wani ɓangare na shari'a ke gabatarwa kai tsaye ga alkali domin ya duba ta ba tare da an bayyana abubuwan da ke cikinta ga sauran ɓangarorin shari'ar ko jama'a ba.
FBI ta fadi dalilin ɓoye bayanan
FBI ta ce ta yi amfani da wasu tanade-tanaden dokar FOIA wajen hana sakin wasu bayanan da aka nema dangane da binciken da ya shafi Tinubu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwafin takardar FBI ya bayyana cewa hukumar ta yi amfani da wani tsari daga FOIA, ciki har da sashe na 6, 7(C), 7(D), 7(E) da 7(F).
Hukumar ta ce wasu daga cikin bayanan da aka riƙe idan aka bayyana su, za su iya tona “dabaru da hanyoyin da jami'an tsaro ke amfani da su wajen gudanar da bincike”.
Ta kuma ce bayyana wasu bayanan na iya jefa rayuwar wani mutum ko lafiyarsa cikin haɗari.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito: An gano bashi ya yi wa Amurka katutu yayin da ta ke yaki da Iran
Bayanan da aka nema kan Tinubu
A cikin takardar, FBI ta bayyana cewa ɗaya daga cikin buƙatun bayanan da aka gabatar mata ya nemi cikakken fayil ɗinta da ya shafi Bola Ahmed Tinubu, wanda aka bayyana ranar haihuwarsa da 29 ga Maris, 1952.
Wata buƙata kuma ta nemi bayanan tambayoyin FBI da aka yi wa Tinubu tsakanin shekarun 1992 zuwa 1993, dangane da wani fayil na bincike mai lamba 245-IP-71386-UUUUUU.

Source: Getty Images
A baya-bayan nan, Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta nemi ƙarin kwanaki 10 domin mayar da martani kan umarnin kotu da ya shafi sakin bayanan da suka shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka danganta da Tinubu.
Sai dai Alkalin Kotun, Beryl Howell, ta amince da ƙarin kwanaki huɗu kacal, zuwa ranar 21 ga Agusta.
Tinubu ya caccaki Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, sun samu saɓani kan batun dawo da tallafin man fetur.
Tinubu ya bayyana cewa Atiku yana nuna rashin fahimta kan harkokin mulki da tattalin arziki ne saboda alƙawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027.
Atiku kuwa ya bayyana wani sabon tsarin tallafin man fetur da ya ce zai maye gurbin tsohon tsarin tallafin shigo da mai da wani tsari na tallafa wa matatun mai na cikin gida.
Asali: Legit.ng

