An Fara: Peter Obi Ya Bude Kamfen, Ya Jefo Kalubale ga Tinubu, Atiku
- Peter Obi ya kalubalanci dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da su fito gaban ’yan Najeriya su kare tarihin ayyukansu
- Ɗan takarar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya ce masu neman shugabancin ƙasa su gabatar da tsare-tsarensu kai tsaye ga jama’a
- Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso sun yi alkawarin zagayawa faɗin Najeriya domin sauraron koke-koken ’yan ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya kalubalanci dukkan masu neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.
Peter Obi ya kalubalance su da su fito gaban jama’a domin kare tarihin ayyukansu da gabatar da tsare-tsarensu ga ’yan ƙasa.

Source: Facebook
Obi ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a hukumance, cewar rahoton jaridar Leadership.
Wane kalubale Peter Obi ya yi?
Ya ce duk wanda ke son jagorantar ƙasar dole ne ya kasance a shirye ya fuskanci ’yan Najeriya tare da barin jama’a su tantance manufofinsa.
A cewar tsohon gwamnan na jihar Anambra, ’yan takarar shugaban ƙasa bai kamata su ɓuya bayan ’yan siyasa ko wakilai ba yayin da suke neman ƙuri’un ’yan Najeriya.
“Dole ne kowane ɗan takara ya kasance a shirye ya gabatar da cancantarsa, ya kare tarihin ayyukansa, sannan ya bar jama’a su yi masa tambayoyi kan manufofinsa."
“Bai kamata wani ɗan takara ya ɓuya a bayan katangar ƙarfin iko, ya tura wakilai ko masu magana a madadinsa, sannan ya yi tsammanin ’yan Najeriya za su amince su ba shi amanar jagorancin ƙasarsu ba."
“Kowane ɗan takara da ke neman shugabancin ƙasa dole ne ya kasance da ƙarfin gwiwar zuwa gaban jama’a, ya amsa tambayoyinsu, ya kare tarihin ayyukansa, sannan ya bar su su tantance manufofinsa.” In ji shi.
Obi ya jaddada muhimmancin tausayi
Obi ya kuma jaddada cewa shugabanci na buƙatar tausayi da hulɗa kai tsaye da jama’a, musamman mutanen da matsalar rashin tsaro da bala’o’in annoba ko na yanayi suka shafa a sassan ƙasar.
Ya ce ba zai yiwu shugaba ya iya gudanar da mulkin jama’a yadda ya kamata ba tare da ziyartar al’ummomin da ’yan bindiga, ’yan ta’adda, masu aikata laifuka da ambaliyar ruwa suka lalata ba.
“Ba za ka iya jagorantar jama’a da gaske ba idan ba ka shirya ziyartarsu, sauraron su da fahimtar halin da suke ciki ba,” in ji shi.
Obi da Kwankwaso za su zagaya Najeriya
Ɗan takarar NDC ya yi alkawarin cewa shi da abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, za su kai yaƙin neman zaɓensu kai tsaye ga ’yan Najeriya a faɗin ƙasar, maimakon dogaro da jami’an jam’iyya ko masu magana da yawunsu.
“Yau, ina yin cikakken alkawari cewa ni da Sanata Rabiu Kwankwaso za mu kai saƙonmu kai tsaye ga ’yan Najeriya. Za mu saurare su, mu fahimci damuwarsu, sannan mu yi hulɗa da su a fili. Ba za mu damƙa wannan aikin ga wani ba."
“Za mu amsa tambayoyinsu, mu kare tarihin ayyukanmu da halayenmu, sannan mu gabatar da shirinmu na sake gina Najeriya.” In ji shi.

Source: Facebook
Peter Obi ya ba 'yan siyasa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya bukaci masu ruwa da tsaki a siyasa su tabbatar da cewa babu dan Najeriya da ya rasa ransa saboda zabe.
Peter Obi ya kuma yi kira ga ’yan takara su gudanar da kamfen bisa batutuwa gabanin babban zaben 2027.
Asali: Legit.ng


