Saudiyya Ta Zauna da Najeriya da Wasu Ƙasashe 74 game da Hajjin 2027
- Saudiyya ta fara taron shirye-shiryen Hajjin 2027 da ofisoshin kula da aikin Hajji na kasashe sama da 75, ciki har da Najeriya
- Saudiyya ta sanya 26 ga Satumba 2026 a matsayin wa'adin karshe da kasashe za su kammala rajistar maniyyatan Hajjin 2027
- Ana sa ran fara isowar maniyyata Saudiyya daga 8 ga Afrilu 2027, yayin da aikin Hajjin zai fara 14 ga Mayu, bisa ga ganin watia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Saudi Arabia – Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fara gudanar da tarukan shirye-shirye da ofisoshin kula da aikin Hajji na sama da kasashe 75.
Daga cikin wadanda aka tattauna da su har da Najeriya, domin tabbatar da an gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin sauki ba tare da tsaiko ba.

Kara karanta wannan
Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

Source: Getty Images
Arab News ta kawo labarin cewa ma'aikatar ta ce tarukan na daga cikin matakan fara shirye-shirye tun da wuri domin inganta hadin gwiwa da daidaita ayyuka.
An fara shirin aikin Hajji
Tribune Online ta wallafa cewa ana yin tarukan domin tabbatar da shirye-shiryen karbar maniyyata da saukaka musu tafiya zuwa Saudiyya domin gudanar da ibadar Hajji a shekara mai zuwa.
A cewar ma'aikatar, tarukan sun mayar da hankali kan shirye-shiryen Hajji da kuma duba tsare-tsaren gudanar da aikin da ofisoshin kula da aikin Hajji suka gabatar.
An kuma tattauna muhimman ka'idoji da dokokin da ke jagorantar gudanar da aikin Hajji, bukatun ofisoshin kula da aikin Hajjin kasashe daban-daban da kuma amsa tambayoyinsu domin kammala dukkan shirye-shirye cikin wa'adin da aka kayyade.

Source: Twitter
Ma'aikatar ta ce:
“Tarukan na daga cikin shirye-shiryen farko na Hajjin 1448 bayan Hijira, bisa umarnin shugabanci na tattara dukkan albarkatun da ake da su domin yi wa maniyyata hidima da saukaka musu tafiya.”
Dalilin fara shirin aikin Hajji da wuri
Ta kara da cewa shirye-shiryen sun yi daidai da manufofin shirin Saudiyya na 2030 da da kuma kokarin inganta ayyuka kan mahajjata ta hanyar karfafa hadin gwiwa tsakanin ofisoshin kula da aikin Hajji da hukumomin da abin ya shafa.
Ma'aikatar Hajji ta Saudiyya ta sanar da fara shirye-shiryen Hajjin 2027 ne a ranar 29 ga Mayu, bayan rufe aikin Hajjin 2026, inda ta fitar da jadawalin gudanar da aikin Hajjin na shekara mai zuwa.
A cikin jadawalin, Saudiyya ta sanya ranar 26 ga Satumba 2026 a matsayin wa'adin karshe da kasashen da za su tura maniyyata za su kammala rajistar su.
Musulmai miliyan 1.7 sun yi aikin Hajji
A baya, kun ji cewa hukumar ƙididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata miliyan 1.7 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2026, adadin da ya zarce na 2025.
Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya sun gudanar da ibadu a Arafah, Muzdalifah da Mina cikin tsauraran matakan tsaro domin kiyaye lafiyar jama'a.
Wasu mahajjata sun bayyana aikin Hajjin a matsayin aikin da ake yi cikin tsananin zafi, amma mai cike da shauki na samun kusanci da Allah Madaukakin Sarki.
Asali: Legit.ng
