Latest
Hedikwatar Tsaro ta ce sojoji sun ceto mutane 59 tare da kashe ’yan ta’adda 11 a samamen da suka gudana a faɗin ƙasar tsakanin 14 zuwa 20 ga Agusta, 2026.
Gwamna Dikko Radda ya ce jiragen yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya sun zama babban abin tsoro ga 'yan bindiga da 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma.
Kungiyar Bola Tinubu 2027 ta bukaci a kama Dino Melaye kan kalamansa cewa abin da ya faru a Venezuela zai faru a Najeriya, tana neman a bincike shi.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya taya Maryam Dan'azumi ta Gombe murnar lashe gasar Alƙur'ani ta duniya, yana yabawa hazakar 'ya'ya mata.
Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta kama baƙin haure 55 ’yan kasashen Kamaru da Kongo a Osun bisa zargin shiga jihar ba tare da takardun izini ba.
Tattaunawar kasuwanci tsakanin kasashen Amurka da Kanada ta rushe, yayin da harajin kashi 50% ya fara aiki kan kayayyakin Kanada na dala biliyan 20.
Jam'iyyar APC ta kafa majalisar yakin neman zaben shugaban kasa, inda Bola Tinubu ke jagoranta, Abdulaziz Yari a matsayin DG, Hope Uzodimma kuma Sakatare.
Wasu mazauna jihar Jigawa sun ce cire tallafin fetur ya ƙara talauci da tsadar rayuwa, yayin da suka goyi bayan Atiku kan alƙawarinsa na dawo da tallafin.
Aƙalla mutane 24 ne aka kashe a harin ’yan bindiga a Bin-Per, Mangu, inda aka shiga gidaje ana harbin mutane da ke barci tare da lalata gidaje da gonaki.
Masu zafi
Samu kari