Sunayen Mutum 20 da ke Jagorantar Sabuwar Hukumar Bogi a Jihohin Najeriya

Sunayen Mutum 20 da ke Jagorantar Sabuwar Hukumar Bogi a Jihohin Najeriya

  • Rahotannin da suka fito sun nuna cewa ana zargin wata hukumar bogi da samun tsari mai rassa a jihohi 20 da kuma kasashen China da Amurka
  • Shafin yanar gizon hukumar ya bayyana George Buchi Nwabueze a matsayin babban darakta na kasa, tare da daraktoci da masu kula da jihohi
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin kama Nwabueze tare da dakatar da sakatarorin gwamnati kan hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Wasu bayanai sun bayyana yadda wata hukumar bogi ta NBDMN ta samar da tsari mai yalwa a jihohi daban-daban na Najeriya da ma kasashen waje.

Rahoto ya nuna nuna cewa shafin yanar gizon hukumar ya lissafo wani mutum mai suna Hon. Nwabueze George a matsayin shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke jami'in DSS na bogi yana barazana da bindigar karya

Shugaban ma'aikatar bogi
Ofishin ICPC da wanda ake zargi da kafa ma'aikatar bogi. Hoto: MAde In Nigeria Project|ICPC
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa hukumar na da daraktan gudanarwa na kasa, daraktocin shiyya uku, masu kula da jihohi 20 da kuma wakilai a kasashen Amurka da China.

Shugaban hukumar da ake zargi

Wannan bayani ya zo ne bayan Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Musa Aliyu, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kama George Buchi Nwabueze.

ICPC ta bayyana Nwabueze a matsayin wanda ya kafa ko kuma yake jagorantar hukumar da ake zargin tana gudanar da ayyuka ba tare da sahalewar shugaban kasa ba.

An kuma gano cewa mutumin yana amfani da sunaye daban-daban, ciki har da George Nathan Nwabueze, George Buchi Nwabueze, Prince George Buchi Nwabueze da kuma George Nwabueze.

An gano masu kula da jihohi 20

Rahoton ya nuna cewa hukumar da ake zargi ta nada masu kula a jihohi 20 na Najeriya, wadanda suka hada da Katsina, Kaduna, Delta, Kebbi, Osun da Anambra.

Kara karanta wannan

Yadda walkiya ta fado kan mata mai ciki ta mutu har lahira a Bauchi

Sunayen da suke shafin hukumar su ne:

  1. Dr Babangida Kabir Ruma — Katsina
  2. Hon. Abdulhaleem Ishaq Ringim — Kaduna
  3. Hon. Dr Godwin Adolor — Delta
  4. Hussaini Abdullahi, Esq., FSI — Kebbi
  5. Hon. Olugbemi Adetola Adelowokan — Osun
  6. Hon. Chiamaka Nnake — Anambra
  7. Hon. Osolafia Muhammed, PhD — Nasarawa
  8. Mrs Salome Audu Bidda — Plateau
  9. Hon. Orduen Andrew Ikon — Benue
  10. Amb. Orioye G. Benedict — Ondo
  11. Hon. Engr. Kehinde Akintonide, FNSE — Ogun
  12. Hon. Ibrahim Umar Aliyu — Sokoto
  13. Hon. Mrs Nwosu Chinyere R. — Abia
  14. Hon. Ibrahim Bello Marafa — Zamfara
  15. Haj. Zainab Mohammed — Niger
  16. Hon. Abubakar Ahmad Bichi (Khalifa) — Kano
  17. Hon. Justin Aondoaseer Tyopuusu — Taraba
  18. Alhaji Bello Kolawole Ghaffar, FCA — Oyo
  19. Hon. Farouq Siyi — Bauchi
  20. Hon. Olorukooba Bidemi — Kogi
Ofishin hukumar ICPC
Wani sashe da ofishin hukumar ICPC a Najeriya. Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Tinubu ya ce a dauki mataki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bayyana cewa ta gano wata hukumar bogi da ke aiki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Ruwan koguna na shirin ɓallewa ya afka cikin Kaduna, Jigawa da wasu jihohi

ICPC ta ce ana zargin George Buchi Nwabueze da kafa ko tallata hukumar tare da zargin hadin gwiwar wasu manyan jami'an gwamnati a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ICPC, Dr Musa Adamu Aliyu, SAN, ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng