Yadda Talakawa ke Komawa Bayan Atiku saboda Dawo da Tallafin Mai
- Wasu mazauna jihar Jigawa sun goyi bayan alƙawarin dan takarar ADC, Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓen 2027
- Mazaunan sun ce cire tallafin ya ƙara tsadar sufuri, abinci da sauran abubuwan more rayuwa, lamarin da suka ce ya jefa talakawa cikin mawuyacin hali
- Sun bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan matakin cire tallafin man fetur da kuma alƙawarin ɗan takarar ADC na dawo da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa – Wasu mazauna jihar Jigawa sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, kan alƙawarinsa na dawo da tallafin man fetur.
Mazaunan sun ce cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi ya ƙara tsananta rayuwa, musamman ga talakawa da masu ƙananan sana’o’i.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yadda yan bindiga suka rika tashin mutane daga barci, su harbe su har lahira

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa batun ya mamaye tattaunawa a wuraren shan shayi, kasuwanni, tashoshin mota da kafafen sada zumunta a jihar Jigawa a kwanakin nan.
Korafi kan tallafin man fetur
Atiku ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, yana mai cewa cire tallafin ya gaza kawo sauƙi ga talakawa.
A cewar mazaunan Dutse da suka yi magana a ranar Juma’a, halin da ake ciki ya nuna cewa cire tallafin ya ƙara wa talakawa nauyin rayuwa.
Malam Musa, wani direba mai shekaru 52 da ke aiki a tashar motar Dutse, ya ce Atiku ya faɗi abin da yawancin talakawan Najeriya ke jira.
Ya ce:
“Kafin cire tallafin, rayuwa da sauki. Yanzu muna cikin wahala. Atiku ya faɗi gaskiyar abin da kowane talaka yake ji. Fetur ya kasance N195, yanzu ya wuce N1,300. Ta yaya za mu rayu?”
Tsadar fetur ya shafi sana'o'insu
Harira Danladi, wadda ke sayar da kayan abinci a kasuwar Dutse ta ce sana'arta na fuskantar matsala saboda rashin kuɗin da jama'a ke da shi.
Ta ce cire tallafin ya kamata ya kawo ci gaba, amma abin da talakawa suka gani shi ne ƙarin wahala.
“Sun ce cire tallafin zai kawo ci gaba, amma abin da muke gani shi ne wahala. Talakawa ne ke biyan kuɗin yayin da manyan mutane suke morewa. Ina goyon bayan Atiku dari bisa dari ya dawo da shi,”
In ji ta.
Usman Shehu, wani matashi mai shekaru 29 a unguwar Takur, ya ce alƙawarin Atiku na nuna cewa ya fahimci halin da talakawa ke ciki.
“Fetur ya shafi rayuwa a Najeriya. Idan ka taɓa fetur, ka taɓa komai. Atiku yana son ya taɓa rayuwar talakawa ta hanyar dawo da tallafin,”
In ji Shehu.
Ma'aikaci ya soki Tinubu
Wani mazaunin jihar, Malam Ibrahim Maibargo, ma'aikacin gwamnati, ya ce kare cire tallafin da Tinubu ke yi ya nuna abin da ya kira rashin tausayi ga talakawa.
Ya ce duk da cewa gwamnati ta ce ba za a koma baya kan cire tallafin ba, talakawa na fuskantar matsin rayuwa.
“Tinubu ya ce babu komawa baya, amma mu talakawa muna cewa babu ci gaba da wannan wahalar. Albashi bai canza ba, amma fetur ya tashi sosai,”
In ji Maibargo.

Source: Getty Images
Haka kuma, Grace John, wata mai sana'ar gyaran gashi a Dutse, ta ce mata masu ƙananan sana'o'i na daga cikin waɗanda suka fi fuskantar matsalar.
Ta ce tana kashe wani kaso mai yawa na ribarta wajen sufuri da sayen man fetur da take amfani da shi.
Legit ta tattauna da dan Gombe
A wata tattauna da da wani mazaunin Gombe, Muhammad Abubakar, ya bayyana cewa yana farin ciki da maganar da Atiku ya yi.
Ya bayyana cewa:
"Dole za mu so dawo da tallafin mai saboda ya shafi rayuwar mu baki daya.
"Saboda haka za mu goyi bayan Atiku Abubakar domin samun saukin rayuwa a Najeriya."
Tinubu ya soki Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya zargi Atiku Abubakar da nuna “ƙarancin fahimta sosai” kan harkokin mulki kan batun maido tallafin mai
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, inda ya soki ra'ayin dawo da tsarin tallafin.
Wasu jami'an gwamnatin Tinubu ma sun yi suka kan alƙawarin Atiku, suna masu cewa dawo da tallafin man fetur a halin yanzu ba dace ba.
Asali: Legit.ng


