Kotun Amurka Ta Dauki Mataki kan Neman Sakin Takardun Zargin Tinubu
- Wata kotun tarayya a Amurka ta amince FBI ta gabatar da wasu bayanan bincike da suka shafi Shugaba Bola Tinubu ga alkali domin a duba su a sirrance
- FBI ta ce ba za ta iya bayyana wasu dalilan rike bayanan a bainar jama'a ba saboda hakan na iya bayyana dabarun bincike ko jefa rayukan wasu mutane cikin hadari
- Alkalin kotun, Beryl Howell, ta bai wa FBI, DEA, DOJ da tawagar lauyoyin Tinubu wa'adin ranar 28 ga Agusta, 2026, domin gabatar da hujjojinsu na karshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Wata kotun tarayya a Amurka ta dauki wani sabon mataki a shari'ar neman a bayyana bayanan bincike da hukumomin kasar suka taba gudanarwa da suka shafi Bola Ahmed Tinubu.
Alkalin Kotun Tarayya ta Amurka da ke Columbia, Beryl Howell, ta amince da bukatar Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka, wato FBI, na gabatar da wasu muhimman bayanai a sirrance domin kotu ta duba su.

Source: Facebook
Bayanai kan wannan sabon mataki sun fito ne daga sakon da Von Batten-Montague-York ya fitar a X, wani kamfanin masu fafutukar kare muradun siyasa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dauki hayarsa.
Dalilin fitar da bayanan a sirrance
FBI ta gabatar da bukatar gabatar da wata sanarwa ga kotu ba tare da bayyana ta ga sauran jama'a ba, a karkashin wani tsari.
Hukumar ta bayyana cewa ba za ta iya bayyana dalilan da suka sa ta rike wasu daga cikin bayanan a bainar jama'a ba.
A cewar FBI, bayyana wasu bayanan na iya tona dabaru da hanyoyin da hukumomin tsaro ke amfani da su wajen gudanar da bincike.
Tribune ta wallafa cewa hukumar ta ce bayyana wasu bayanan na iya haifar da barazana ga rayuwa ko lafiyar wasu mutane.
Sabon wa'adin da kotu ta sa
A cikin umarninta, Alkaliya Beryl Howell ta umarci FBI, Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Amurka (DEA), Ma'aikatar Shari'a ta Amurka (DOJ) da kuma tawagar lauyoyin Shugaba Tinubu su gabatar da hujjojinsu na karshe.
Kotun ta sanya ranar 28 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar karshe da bangarorin za su gabatar da matsayinsu kan batun ko za a bayyana bayanan ga jama'a.
Kamfanin Von Batten-Montague-York ya ce akwai alamun da ke nuna cewa umarnin kotun na nuna cewa alkalin na son a gaggauta kammala wannan doguwar takaddama.
Kamfanin ya kuma yi ikirarin cewa amincewar kotun ta duba wasu bayanai a sirrance na nuna cewa akwai wasu bayanan tsaro masu muhimmanci da FBI ba za ta iya bayyana su a bainar jama'a ba.
Kwamitin kamfen din Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya kafa Kwamitin Yakin Neman Zabensa na jam'iyyar APC gabanin babban zaben shekarar 2027.
Tinubu ya nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar na kwamitin, yayin da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, zai zama sakatare.
Shugaba Tinubu ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, za su kasance a ciki.
Asali: Legit.ng

