Ana Wata ga Wata: An Kama Yan Kasashen Waje da Suka Shigo Najeriya Ta Barauniyar Hanya

Ana Wata ga Wata: An Kama Yan Kasashen Waje da Suka Shigo Najeriya Ta Barauniyar Hanya

  • Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta kama baƙin haure 55 ’yan Kamaru da Kongo da suka shigo Najeriya ba bisa ka'ida ba
  • Hukumar NIS ta bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka kama na gudanar da sana’ar intanet ba bisa ƙa’ida ba
  • An kama su ne bayan samun bayanan sirri kan wuraren da suke zaune a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS), reshen Jihar Osun, ta baƙin haure 55 da ta kama a wurare daban-daban a jihar a ranar Juma’a a Osogbo.

Hukumar ta ce baƙin hauren ’yan ƙasar Kamaru da Kongo ne, kuma sun shiga jihar ba tare da takardun da suka dace ba.

NIS .
Jami'an hukumr shige da gice ta Najeriya suna faretin girmamawa a hedkwatar NIS da ke Abuja Hoto: NIS Nigeria
Source: Twitter

Punch ta ce da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan gabatar da su, Kwanturolan Hukumar Shige da Fice na Jihar Osun, Ibrahim Akinyemi, ya ce an kama yan kasar wajen ne bisa bayanan sirri da hukumar ta samu.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun bindige dan bindiga har lahira a wani artabu da suka yi

Yadda aka kama bakin haure a Osun

Akinyemi ya ce baƙin hauren sun kai kusan 55 kuma ana shirin mayar da su ƙasashensu bayan kammala tantance su.

“Waɗannan mutane kusan 55 ne. Baƙin haure ne da ba su da cikakkiyar takardar zama. An kama su kuma an kawo su nan domin mayar da su ƙasashensu.
"Sun shigo ne ta wata hanya da ba a amince da ita ba. Saboda haka, zamansu a nan ya zama babbar matsala,” in ji shi.

Ya ce hukumar ta gano wuraren da suke zaune ne ta hanyar tattara bayanan sirri, sannan ta kama su bisa umarnin hedikwatar hukumar ta hanyar Kwanturolan-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.

Jami'an NIS sun tattara bayanai

Ya ce hukumar za ta tantance takardunsu domin gano waɗanda suka cancanci zama a Najeriya bisa doka da kuma waɗanda za a iya ba su damar daidaita matsayinsu.

Kwanturolan ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa baƙin hauren ba su da takardun tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

“Ba su ma da fasfo na yau da kullum, kuma suna nan suna gudanar da wannan sana’ar intanet ba bisa ƙa’ida ba wadda ba a yi mata rajista da Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ba,” in ji shi.

Akinyemi ya ƙara bayyana cewa an kama wasu daga cikinsu a yankin Owode-Ede, yayin da hukumar ke ci gaba da neman wasu da ka iya fakewa a wuraren da ba a gano su ba a faɗin jihar.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bakin hauren sun ambaci QNET

Akinyemi ya ce yayin da ake yi musu tambayoyi, baƙin hauren sun bayyana cewa sun zo jihar ne domin gudanar da wani kasuwancin intanet mai suna QNET.

Sai dai ya ce sun ƙi bayyana ƙarin bayani kan irin wannan kasuwancin, amma ya ce hukumar za ta bibiyi mutanen da suka taimaka wajen shigo da baƙin hauren jihar.

Za dauki jami'in NIS da hukumomi 3

A wanj labarin, kun ji cewa hukumar CDCFIB ta ce za ta kammala daukar sababbin ma’aikatan hukumomin NSCDC, NIS, NCoS da Fire Service cikin makonni hudu.

Sanarwar ta zo ne bayan dogon lokaci da dubban matasa marasa aikin yi suka shafe suna jiran kammala aikin daukar ma’aikatan da ya shafi wadannan hukumomi hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262