Gwamna Radda Ya Fadi Makamin Najeriya da 'Yan Bindiga ke Jin Bala'in Tsoro

Gwamna Radda Ya Fadi Makamin Najeriya da 'Yan Bindiga ke Jin Bala'in Tsoro

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana daya daga cikin makaman da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifi suka fi tsoro a yankin Arewa maso Yamma
  • Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, ya ce jiragen yakin NAF na taka muhimmiyar rawa wajen kai hare-hare a wuraren da 'yan bindiga ke boye
  • Hakan na zuwa ne yayin da rundunar ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da kai munanan hare-hare kan 'yan bindiga da 'yan ta'adda a Katsina da Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana jiragen yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) a matsayin daya daga cikin makaman da 'yan ta'adda da 'yan bindiga suka fi tsoro a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Kalubalen da ke gaban Atiku kan maganar dawo da tallafin mai idan ya yi nasara

Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da Babban Jami'in Ayyuka na Rundunar Sojin Sama, Air Vice Marshal PN Amadi, ya kai ziyarar aiki ga bangaren rundunar da ke karkashin Operation Fansan Yamma a jihar Katsina.

Wasu sojojin Najeriya a Katsina
Dakarun Najeriya tare da jiragen yaki. Hoto: NAF
Source: Facebook

A wata sanarwa da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta fitar a Facebook, ta ce Radda ya yaba da irin gudunmawar da NAF ke bayarwa wajen yakar rashin tsaro, musamman yadda jiragenta ke kai farmaki zuwa wuraren da ke da wahalar shiga.

Makamin da 'yan ta'adda ke tsoro

Gwamna Radda ya ce amfani da karfin jiragen yakin rundunar na taimakawa wajen raunana karfin 'yan ta'adda da 'yan bindiga tare da hana su damar gudanar da ayyukansu cikin walwala.

Ya yaba da sadaukarwar jami'an Rundunar Sojin Sama wajen yaki da matsalolin tsaro da suka addabi Katsina da sauran jihohin yankin Arewa maso Yamma.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar Katsina za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa daga sama da kuma kasa.

Gwamna Radda da sojoji
Gwamnan Katsina tare da wasu sojojin Najeriya. Hoto: NAF
Source: Facebook

NAF ta jaddada aniyar kai hari

A nata bangaren, Air Vice Marshal PN Amadi ya sake jaddada kudurin Rundunar Sojin Sama na ci gaba da tsananta hare-hare kan 'yan ta'adda, 'yan bindiga da sauran masu aikata laifi a Katsina da sauran yankunan Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka kan masu sallar Juma'a, sun saci adadin mutane mai yawa

Ya ce hadin kai tsakanin rundunonin tsaro, sauran hukumomin tsaro, gwamnatoci da al'ummomin yankunan da abin ya shafa na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Ziyarar ta kuma jaddada manufar Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, na tabbatar da walwala, shiri da kuma ingancin aikin jami'an da ke kan gaba wajen yaki da rashin tsaro.

Sojoji sun bindige dan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun ceto wani mutum da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna tare da dakile wani hari a jihar Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun amsa kiran gaggawa bayan da aka sace wani mutum mai shekaru 43 a yankin Awon da ke karamar hukumar Kachia a ranar 20 ga Agusta, 2026.

Dakarun sun bi 'yan ta'addan zuwa cikin dazuka, lamarin da ya tilasta musu barin wanda suka sace kafin su tsere da kuma harbe daya daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng