Cibiyar BBYDI Za Ta Horar da Mata kan Ilmin Amfani da Fasahar AI a Kaduna
- Shirin 'SheBuilds AI Fellowship' zai dauki tsawon wata shida yana koya wa mata ilmin AI a garin Kaduna
- Gwamnatin kasar Kanada ce ta dauki nauyin shirin ta hanyar asusun CFLI da BBYDI domin taimaka wa mata
- Rububin ya nuna matan Arewa suna da sha'awar fasaha, inda aka samu mutane 473 da suke sha’awar shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Wata cibiya mai zaman kan ta, BBYDI za ta horar da mata a kan abin da ya shafi ilmin AI da yake tashe a duniya.
Shirin zai koyar da matan dabarun kirkirarriyar fasaha, kimiyyar bayanai da salon kasuwanci na zamani a karkashin shirin CFLI.

Source: UGC
Gwamnatin Kanada ta taimaka wa mata wajen AI
Bayanan da Legit Hausa ta samu daga cibiyar BBYDI ya ce Gwamnatin Kanada ta fito da CFLI domin inganta rayuwar matasa.

Kara karanta wannan
Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa
Shugaban BBYDI a duniya, Olasupo Abideen Opeyemi, ya shaida cewa mutane 473 suka nuna sha’awar samun wannan horo.
A karshe sun kira mutane 52 aka yi masu tambayoyi, kuma aka zakulo mutane 20 da za a shafe watanni shida ana horar da su.
Maza sun yi wa mata nisa a Najeriya
An kawo horon ne domin kokarin bunkasa tattali da kuma rage gibin ilimin na'ura mai kwakwalwa da ake da shi tsakanin mata da maza.
Ganin mutane 473 suka nemi gurbin da za a dauki mutane 20 kacal, Olasupo Abideen ya ce hakan ya nuna irin sha’awar matasan.
Ya ce wannan ya karyata tunanin da wasu suke yi cewa mata a yankin Arewacin Najeriya ba su damu da harkokin fasahar zamani ba.
An fahimci babu rashin sha’awar fasahar wajen mata, illa dai matsalar da ake fuskanta ita ce ta karancin irin wadannan damammaki.
Karin matsalolin da mata ke fuskanta

Kara karanta wannan
APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa
A yau a Najeriya, har adadin mata masu amfani da yanar gizo bai kai na maza ba, kuma an yi masu nisa wajen ayyukan fasaha a kasar.
Ba a nan kadai ba, ana tunanin cewa mata miliyan 70 sun fuskanci tsangwama da cin mutunci da aka yi masu da fasahar AI a yanar gizo.
Ganin irin haka, shugaban kuniyar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na Kaduna su sa irin wannan darasi a cikin shirin 3MTT da aka kawo.
Ya kuma bukaci Majalisa ta yi dokokin da za su yi maganin cin mutuncin mata a kafafen yanar gizo.

Source: Original
Wannan tazara da maza suka ba mata ya yi nisa sosai, masana suka ce idan aka cigaba da tafiya a haka, za a samu mummunar matsala.
Saboda haka ne Kanada ta ɗauki nauyin gudanar da wannan shiri ta hanyar gidauniyar CFLI domin tallafa wa musamman ‘ya ‘ya mata.
Nan gaba kadan kuma ya ce za a sake daukar wasu matasa 20 da za a ba wannan horo. Jaridar nan The Nation ta fitar da labarin a jiya.
Abideen ya mika godiya ga Gwamnatin Kanada da ofishin jakadancin kasar na Najeriya da suka sa kudinsu wajen ilmantar da matasa.
FactCheckAfrica ta horar da matasa kan labaran bogi
Ana da labarin wani taron karawa juna sani da kungiyoyin FIAP da FactCheckAfrica suka shirya a birnin Kano domin yaki da labaran karya.
An shirya taron ne karkashin taken #CheckBeforeYouPost domin tsabtace shafukan sada zumunta daga labaran bogi da kuma na kiyayya.
An zabi matasa da mata guda 30 daga jihohin Arewa kamar Kano, Kaduna, Jigawa, Sokoto, Kwara, Neja, Nasarawa, da Filato, aka horar da su.
Asali: Legit.ng
