Melaye Ya Kira Ruwa bayan Cewa Abin da Ya Faru a Venezuela Zai Iso Najeriya
- Kungiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu 2027 Forum ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su kama tsohon Sanata Dino Melaye
- Ta ce kalaman Melaye cewa abin da ya faru a Venezuela zai faru a Najeriya na iya jawo barazana ga tsaron kasa
- Ƙungiyar ta ce duk da cewa suka da adawa da gwamnati halas ne a dimokuradiyya, bai kamata a yi kalaman da za su iya jawo tsoma bakin kasashen waje ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata kungiyar siyasa mai suna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu 2027 Forum ta bukaci a kama tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan kalaman Melaye, tana gargadin cewa maganar na iya shafar tsaron kasa.

Kara karanta wannan
Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Source: Facebook
Kalaman Melaye da suka ta da hazo
Melaye ya wallafa a shafinsa na X da aka tantance ranar Laraba cewa abin da ya faru a Venezuela zai iya faruwa a Najeriya.
Ya kuma bukaci Shugaba Bola Tinubu ya bar mulki bayan kammala zaben shugaban kasa na 2027, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.
Kungiyar NDI-ABAT ta bayyana kalaman a matsayin masu tayar da hankali da rashin kishin kasa, tana mai cewa za su iya kara dagula yanayin siyasar Najeriya.
Ta kuma ce kalaman Dino Melaye na iya zama kamar kira ko karfafa gwiwar kasashen waje su tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya.

Source: Facebook
Ƙungiya ta bukaci kama Dino Melaye
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, Mai Gudanar da Kungiyar na Kasa, Mazi Isiguzoro, da Shugaban Kwamitin Amintattu, Dimm Okwukwu, sun ce Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta turje, ta ki fitar da bayanai game da rancen $5bn daga Abu Dhabi
Sun bayyana cewa kasar tana karkashin tsarin hukumomin kundin tsarin mulki da kuma bin doka da oda.
Kungiyar ta jaddada cewa sabanin ra’ayi na siyasa da sukar manufofin gwamnati abubuwa ne halastattu a tsarin dimokuradiyya.
Sai dai ta ce duk wata magana da za ta iya nuna goyon baya ko karfafa tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin Najeriya ya kamata hukumomin da suka dace su bincika.
Saboda haka, NDI-ABAT ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su “arrest Senator Dino Melaye immediately” tare da binciken dalili, manufa da illolin kalaman nasa.
Kungiyar ta ce idan binciken ya tabbatar da cewa Melaye ya karya wata doka a Najeriya, ya kamata a dauki matakin shari’a da ya dace a kansa, cewar Punch.
Ta kuma ce adawa da gwamnati da sukar zababbun jami’ai muhimman abubuwa ne a dimokuradiyya, amma dole ne a yi su cikin mutunci da sanin ya kamata.
Yadda akuya ta zama arzikin Dino Melaye
An ji cewa Dino Melaye ya bayyana cewa ya saye akuya tun yana shekara 12, kuma da haka ya biya kudin karatu a sakandare da ABU Zari.
Ya yi ikirarin fara zuba jari a kasashen waje tun yana karami, ya sa kudinsa a kamfanonin Apple, Microsoft, Uber da kuma Zoom.
Hukumomin yaki da barna irin su EFCC da ICPC ba su taba gayyatarsa ba, Dino ya ce hakan ya tabbatar da bai mallaki kudin sata ba.
Asali: Legit.ng
