Dangote Ya Yi Abin Alheri ga Jami'ar Lagos da Maƙudan Kuɗi, Zai ba Ɗalibai Aiki

Dangote Ya Yi Abin Alheri ga Jami'ar Lagos da Maƙudan Kuɗi, Zai ba Ɗalibai Aiki

  • Attajirin dan kasuwa a Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya bayar da gudunmawar makudan kudi a jami'ar jihar Lagos
  • Kamfanin Dangote zai bai wa ɗaliban LASU da suka kammala karatu da digiri na farko a fannin Injiniya da Kimiyya fifiko wajen samun aikin yi
  • Dangote ya kuma samu lambar girmamawa ta digirin digirgir a fannin kasuwanci, yayin da LASU ta samar da ɗalibai 20,604 a shekarun karatu biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya yi alkawarin bayar da gudunmawar miliyoyi ga jami'ar Lagos.

Dangote ya yi alkawarin ba da N600m domin gina ɗakin kwanan ɗalibai mata a Jami’ar Lagos, LASU.

Dangote zai ba ɗalibai jami'ar Lagos aiki
Attajiri Alhaji Aliko Dangote yana jawabi a taro. Hoto: Aliko Dangote.
Source: Getty Images

Dangote ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai na karo na 29 da 30 da jami’ar ta gudanar a babban harabarta dake Ojo, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin Maulidin Annabi Muhammad SAW

Dangote ya kuma yi tayin samar da guraben aikin yi ga ɗaliban LASU da suka samu digiri na farko a fannonin Injiniya da Kimiyya.

Attajirin, wanda ‘yarsa Fatima Aliko Dangote ta wakilta, ya samu lambar girmamawa ta digirin digirgir a fannin kasuwanci, bunƙasa masana’antu da jari na ɗan Adam.

Bayanin jami’ar ya ce bikin kammala karatun ya zo da manyan alkawura kan jin daɗin ɗalibai, ƙwarewar ilimi da samar da ayyukan yi ga waɗanda suka kammala karatu.

Ya ce ta hannun gidauniyar Aliko Dangote, ɗan kasuwar ya yi alkawarin N600m domin gina ɗakin kwanan ɗalibai mata tare da tallafa wa ƙwararrun ɗalibai.

An bayyana cewa ɗaliban da suka samu digiri na farko a Injiniya da Kimiyya za su samu fifiko wajen neman aiki a kamfanin Dangote bayan kammala bautar ƙasa, NYSC.

Rukunin kamfanonin Dangote na ɗaukar ma’aikata sama da 52,000 a Najeriya da wasu ƙasashe 11 na Afirka, yayin da Dangote Academy ke horas da waɗanda suka kammala karatu.

Gidauniyar Dangote tana gudanar da shirin tallafin karatu, tare da shirin kashe dala miliyan 70 duk shekara na tsawon shekaru 10 kan ilimi da horas da malamai.

Kara karanta wannan

Gombe 2027: Sakon Jamilu Gwamna ga Pantami, ADC ana daf da fara kamfen

Shirin zai kuma shafi fannonin Kimi ukuyya, Fasaha, Injiniya da Lissafi, STEM, da ilimin fasaha da koyar da sana’o’i a makarantun sakandare da manyan makarantu.

Wannan ci gaban ya biyo bayan bayar da N20m ga kowane daga cikin ɗalibai biyu da suka fi kowa ƙwarewa a bikin kammala karatun.

Gwamnan Lagos kuma mai kula da jami’ar, Babajide Sanwo-Olu, ne ya bayar da tallafin N20m ga kowane ɗayan ɗaliban biyu da suka yi fice.

A jawabinsa, Sanwo-Olu ya taya sabbin waɗanda suka kammala karatu, iyayensu, masu daukar nauyinsu da malamansu murna bisa nasarar da suka samu.

Gwamnan ya ce LASU ta samar da waɗanda suka kammala karatu 20,604 a shekarun karatu na 2024/2025 da 2025/2026, ciki har da 494 da suka samu digiri na farko.

Yakin Iran: Ribar da Dangote ya samu

An ji cewa Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya ƙara samun sama da dala biliyan 5 sakamakon karuwar buƙatar man fetur tun bayan barkewar yaƙin Iran.

Matatar man Dangote da ke Legas ta samu karuwar buƙatar kayayyakin man fetur a Afirka da sauran sassan duniya saboda yakin.

Matatar wadda ta kai darajar dala biliyan 20 ta zama ɗaya daga cikin manyan masu fitar da man jiragen sama da dizal zuwa kasuwannin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.