Yadda Hakimi Ya Sha da Ƙyar a Hatsarin Jirgin Ruwa da ya Kashe Mutane Fiye da 60

Yadda Hakimi Ya Sha da Ƙyar a Hatsarin Jirgin Ruwa da ya Kashe Mutane Fiye da 60

  • Hakimin Gorau a jihar Sokoto ya bayyana yadda ya tsira daga hatsarin kwale-kwalen da ya kife a Goronyo, Sokoto, inda mutane da dama suka rasu
  • Dattijon ya ce ruwa ya shiga kwale-kwalen kafin ya kife, yayin da fasinjoji suka riƙe shi, lamarin da ya tilasta masa nutsewa domin ya kuɓuta
  • Ya ce ya samu damar tsira ne bayan ya kama wani buhu, sannan mutane suka taimaka masa zuwa bakin ruwa kafin a kai shi gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Hakimin Gorau, Aliyu Magaji, ya ba da labarin yadda ya tsira daga hatsarin kwale-kwale da ya afku a ƙaramar hukumar Goronyo ta Sokoto.

Hatsarin ya faru ne ranar Alhamis, bayan kwale-kwalen ya cika da ruwa kafin daga bisani ya kife da fasinjojin da ke cikinsa.

Kara karanta wannan

An birne ƴan uwa 11 da wasu mutum 41 bayan kifewar kwale kwale a Sokoto

Mutane fiye da 60 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa
Taswirar jihar Sokoto da aka yi mummunan hatsarin jirgin ruwa. Hoto: Legit.
Source: Original

Hakimin ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo yayin hira da tashar Icon FM wanda wakilin Legit Hausa ya bibiya a shafinta na Facebook.

Hakimi ya fadi yadda ya tsira a hatsarin

Magaji ya bayyana cewa shi ne babban mutum ɗaya tilo a cikin kwale-kwalen baya ga matuƙin jirgin da ke jagorantar tafiyar.

Ya ce lokacin da ruwa ya fara shiga kwale-kwalen, fasinjojin da ke ciki suka yi gaggawar riƙe shi, lamarin da ya hana shi kuɓuta.

A cewarsa, bayan ya kasa kuɓuta daga hannunsu, sai ya nutse tare da su, kafin daga bisani ya zage kayan jikinsa domin ya samu damar tsira.

Magajin ya ce da ya sake bayyana a saman ruwa, wasu daga cikin mutanen suka sake riƙe shi, abin da ya sa ya sake nutsewa.

Daga baya, ya samu damar yin iyo zuwa wani wuri daban, inda ya gano wani buhun tonka da ya taimaka masa wajen kuɓuta daga hatsarin.

Kara karanta wannan

Babban balilin da ya sa Amurka ba za ta cire Najeriya daga jerin kasashen CPC ba

Ya ce da taimakon Allah ya yi amfani da buhun domin ya samu damar isa inda zai iya fita daga cikin ruwan.

Hakimi ya tsira daga hatsarin jirgin ruwa a Sokoto
Hakimin Gorau, Aliyu Magaji da ya sha da kyar a hatsarin jirgin ruwa a Sokoto. Hoto: Iconic FM.
Source: UGC

Hatsarin jirgin ruwa: Yadda aka taimaka wa Hakimi

Bayan ya isa bakin ruwa, wasu mutane suka taimaka masa suka kai shi gefe, inda ya shafe kusan awa ɗaya cikin rashin sanin abin da ke faruwa.

Daga baya, an samu babur da ya kai shi cikin garin, yayin da jikinsa ya fara dawowa hayyacinsa kafin lokacin La’asar.

Hakimin ya ce bayan faruwar hatsarin, an tsamo gawarwakin mutane da dama, inda aka yi jana’izar kusan mutane 48 da farko.

Ya ƙara da cewa daga baya adadin waɗanda aka binne ya kai kusan mutum 62, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci NIWA da NEMA su haɗa kai da gwamnatin Sokoto domin hana sake faruwar irin wannan hatsari.

Ya kuma bukaci hukumomin su tabbatar da cewa ana bin ƙa’idojin tsaro yadda ya kamata a hanyoyin sufuri na cikin ruwa.

Kara karanta wannan

Cutar Apollo ta ɓarke a wasu jihohin Arewacin Najeriya, ta fara yaɗuwa cikin jama'a

Hatsarin ya faru ne shekara guda bayan wani makamancin haka da ya auku a Kijiyo, cikin ƙaramar hukumar Goronyo ta Sokoto.

Yan bindiga: Mazauna Sokoto sun soki gwamnati

An ji cewa yan bindiga sun kashe mutane 32 tare da sojoji huɗu a hare-haren da suka kai yankunan Kebbe da Ungushi a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Sama da mutum 5,000 daga ƙauyukan Ungushi da kewaye sun tsere zuwa Jega a Jihar Kebbi domin neman mafaka tare da neman tsira.

Rundunar Sojoji da Gwamnatin Sakkwato sun ce sun ɗauki matakan ƙara matsa wa ’yan bindiga tare da taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.