Sojojin Najeriya Sun Samu Gagarumar Nasara, Sun Tura Yan Bindiga da Dama Lahira

Sojojin Najeriya Sun Samu Gagarumar Nasara, Sun Tura Yan Bindiga da Dama Lahira

  • Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ya sanar da nasarorin da rundunar sojoji ta samu cikin mako guda a sassa daban-daban na Najeriya
  • DHQ ta bayyana cewa sojoji sun ceto mutane 59 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda tare da kashe ’yan ta’adda 11
  • An gudanar da samamen ne a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da sauran sassan ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta ce dakarun soji sun ceto aƙalla mutane 59 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ’yan ta’adda 11 yayin wasu samame da suka gudanar a faɗin ƙasar tsakanin 14 zuwa 20 ga Agusta.

Daraktan Sashen Yaɗa Labaran Ayyukan Sojoji, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar kan ayyukan sojojin a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun bindige dan bindiga har lahira a wani artabu da suka yi

Sojoji.
Dakarun Sojojin Najeriya yayin da suka fito fagen aiki a Arewa Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Onoja ya ce dakarun Operation HADIN KAI sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas a cikin makon, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Ya ce sojojin sun kuma ceto mutane uku daga dajin Gwamnare a Bauchi da kuma wani ɗan ƙasar Kamaru mai shekaru 63 da aka yi garkuwa da shi a kan hanyar Gwoza zuwa Kamaru.

Sojoji sun murkushe yan bindiga

A cewar Onoja, sojojin sun kuma kashe ’yan ta’adda uku tare da kwato makamai da sauran kayayyakin yaƙi.

Ya ƙara da cewa ’yan uwa 47 na ’yan ta’addan da kuma mayaƙa shida sun miƙa wuya ga sojoji a Jihar Borno.

A yankin Arewa maso Yamma kuwa, Onoja ya ce dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 28 da aka yi garkuwa da su a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto tsakanin 17 zuwa 19 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

Ya ce sojojin sun kuma kashe ’yan ta’adda huɗu, tare da kama wani mai kai kayan fashewa da wasu da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda. An kuma kwato makamai, harsasai, babura da kuɗi yayin samamen.

Onoja ya ce aikin ya kuma kai ga kama wasu mutane shida da ake zargi da kasancewa masu leƙen asiri da ke da alaƙa da sace iyalan wani jami’in shige da fice da kuma ma’aikata da ɗaliban Federal Polytechnic, Kaura Namoda.

Sojoji sun ceto mutane da dama

A Arewa ta Tsakiya, ya ce dakarun Operation WHIRL STROKE sun tilasta wa masu garkuwa da mutane sakin mutane 13 a Jihar Kogi, ciki har da maza biyu, mata biyar da yara shida.

Sojojin sun kuma kashe wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifuka, tare da kama wani mai safarar makamai da kwato bindigar AK-47, harsasai da wasu makamai a wasu samame daban-daban a Taraba da Benue.

Hafsan soji.
Babban hafsan rundunar sojin Najeriya, Janar Oluyede Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

CDS ya yaba wa sojojin Najeriya

Onoja ya ce Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa dakarun bisa ci gaba da samun nasarori wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kashe ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Ya ce Oluyede ya kuma yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin sojoji, sauran hukumomin tsaro da ƙungiyoyin tsaron al’umma.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da shugabannin al’umma su ci gaba da bai wa dakarun bayanan sirri masu amfani, kamar yadda Punch ta rahoto.

Sojoji sun ceto mutum 1 a Kaduna

Kun ji cewa dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun ceto wani mutum da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna.

Jami'an sojojin sun kuma dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai a jihar Sokoto, inda suka kashe ɗaya daga cikin maharan

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262