Khamis Mailantarki: Wane ne Yake Yakar Pantami a PDP wajen Zama Gwamnan Gombe
- Khamisu Ahmed Mailantarki ya ki hakura da zancen neman takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP
- Sai yanzu wasu suke jin sunansa, amma tun shekaru kusan 15 da suka wuce ya zama ‘dan majalisa a Gombe
- Daga CPC, APC, NNPP zuwa PDP, Khamisu Ahmed Mailantarki ya yi yawo tsakanin jam’iyyun siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Khamisu Ahmed Mailantarki yana cikin manyan abokan karawar Isa Ali Ibrahim Pantami tun bayan shigowarsa PDP a 2026.
‘Dan siyasar ya kalubalanci takarar gwamna na 2027 da jam’iyyar PDP ta ba malamin addinin Musuluncin a jihar Gombe.

Source: Facebook
Duk da wasu masu neman takarar sun hakura, sun janye wa Sheikh Isa Ali Pantami, shi Khamis Mailantarki bai hakura ba.
Hon. Mailantarki ya yi kara har aka rusa takarar tsohon ministan kuma yanzu ya fito yana cewa shi yake rike da tutar PDP.
Wannan rahoto ya yi kokarin kawo takaitaccen tarihin rayuwar Mailantarki musamman daga shafinsa na Blerf da Wikipedia.
Takaitaccen tarihin Khamisu Ahmed Mailantarki
1. Haihuwa da karatun Khamis Mailantarki
An haifi Khamisu Ahmed Mailantarki a ranar 19 ga watan Yuni 1975 a rukunin gidaje na Herwagana da ke garin Gombe, jihar Gombe.
Ya shiga firamaren Gombe Township Primary School gabanin tafiya makarantar GSSS Gombe domin yin karatun sakandarensa.
Tribune ta rahoto cewa ya samu digiri a ilmin Geography a jami’ar Uni Abuja a shekarar 2002.
Kafin ya shiga harkar siyasa gadan-gadan, ya yi karatu Federal Technical College, Yabada ke Legas kuma yana da wasu takardu daga Amurka.
2. Hon. Mailantarki a Majalisar wakilan tarayya
A zaben 2011 sunan Khamisu Mailantarki ya zagaya ko ina da ya zama ‘dan majalisar Gombe/Kwami/Funakaye a CPC.
Farin jinin da ya samu a filin zabe ya jawo shahararsa, babu ‘dan majalisar da ya kai shi yawan kuri’u Arewa maso gabas - 139, 000.
Bayan haka shi ne ya wakilci CPC da Muhammadu Buhari wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar.
Ya zarce a kujerar shi amma Kotun koli ta tsige shi, ta ce Yaya Tongo ne asalin wanda ya ci zaben tsaida gwanin APC a mazabarsa.
3. Sauran mukaman da ya rike a gwamnati
Yana cikin manyan kwamitoci kamar na harkokin birnin Abuja, mai, tsaron cikin gida, dumamar yanayi da sauransu a majalisa.
Bayan barin ofis, Mailantarki ya zama cikin majalisar da ke sa ido wajen aikin hukumar ICPC mai yaki da rashawa a Najeriya.
4. Neman takarar gwamnan Gombe
Khamisu Ahmed Mailantarki ya shiga cikin masu son zama gwamnan Gombe a APC a 2019, amma jam’iyyar ba ta ba shi tikiti ba.
Daga baya ya rabu da jam’iyyar APC mai mulki. ‘Dan siyasar ya samu takarar gwamna babu hamayya a NNPP a zaben 2023.
Da ya tashi yin murabus daga jam’iyyar NNPP, sai ya shiga PDP da niyyar sake jarraba sa’arsa wajen zama gwamna a Gombe.
Yanzu haka ana ta fama da shi a jam’iyyar hamayyar, yana adawa da takarar Isa Pantami wanda ya same su bayan barin APC.
5. Harkar kwallon kafa
Mailantarki ne ya kafa kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki Football Care Academy da ke horar da yara masu tasowa a Najeriya.
Kungiyar kwallonsa ta lashe gasar Dana Cup na yara’yan kasa da shekara 19 da aka gudanar a shekarar 2022 a kasar Denmark.

Source: Facebook
Mailantarki ya caccaki Sheikh Pantami
An rahoto Khamisu Mailantarki ya caccaki Farfesa Isa Ali Pantami kan cewa ya yi masuu rashin adalci kuma ya ci musu mutunci a siyasar Gombe.
Mailantarki ya yi ikirarin cewa Pantami ya bar harkar malanta yana neman mabiya, wadanda kusan 95% daga cikinsu ba 'yan jihar Gombe ba ne.
Ya kuma kara da cewa ko da yake malamin ya fi shi ilimin addini, amma shi ya fi sa gogewa a fannin siyasa saboda matsayi da ya rike da takara da ya yi.
Asali: Legit.ng


