Sultan Ya Taya Maryam Dan'azumi Murnar Lashe Gasar Kur'ani Ta Duniya

Sultan Ya Taya Maryam Dan'azumi Murnar Lashe Gasar Kur'ani Ta Duniya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya taya Maryam Ibrahim Dan'azumi murnar lashe gasar Alƙur'ani ta duniya a Saudiyya
  • Sarkin Musulmin ya ce nasarar Maryam ta zama abin alfahari ga Najeriya da daukacin al'ummar Musulmi, tare da nuna hazakar matasan ƙasar
  • Ya kuma ce nasarar Maryam ta kara nuna muhimmancin bai wa 'ya'ya mata ilimi, kulawa da jagoranci domin su cimma manyan nasarori a rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya taya Maryam Ibrahim Dan'azumi ta jihar Gombe murnar lashe gasar Alƙur'ani ta duniya da aka gudanar a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Maryam Dan'azumi ta wakilci Najeriya a gasar Alƙur'ani ta kasa da kasa karo na 46 mai dauke da sunan Sarki Abdulaziz, inda ta zama zakara a bangaren mata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka kan masu sallar Juma'a, sun saci adadin mutane mai yawa

Sarkin Musulmi da Maryam Dan'azumi
Sarkin Musulmi a hagu da Maryam Dan'azumi a dama. Hoto: JNI|Yusuf Muhammad Dukku
Source: Facebook

A wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin Sarkin Musulmi a Facebook, ya bayyana nasarar Maryam a matsayin babban abin alfahari ga Najeriya da daukacin al'ummar Musulmi.

Sultan ya yabi Maryam Dan'azumi

Maryam 'yar asalin jihar Gombe ce kuma daliba a makarantar Abubakar Siddiq da ke unguwar Herwagana a cikin garin Gombe.

Ta fafata ne a bangaren haddar Alƙur'ani mai girma baki daya, karatu da Tajwidi da kuma Tafsiri, wato izu 60 tare da tafsiri.

Sarkin Musulmi ya ce nasarar da Maryam ta samu a wannan gasa mai girma ta nuna irin hazaka da damar da matasan Musulmi na Najeriya suke da ita idan aka ba su dama da ingantaccen jagoranci.

Ya ce abin farin ciki ne yadda Maryam ta daga tutar Najeriya a matakin kasa da kasa tare da samun wannan babbar nasara.

Nasarar Maryam ta dabam ce

A cewar sanarwar, karo na 46 na gasar Sarki Abdulaziz ya kasance karo na farko da aka ba mata damar shiga gasar tun bayan shafe shekaru 46 ana gudanar da ita.

Kara karanta wannan

Maryam Dan Azumi: Abin da Tinubu ya ce kan yarinyar da ta lashe gasar Kur'ani

Sarkin Musulmi ya ce abin farin ciki ne matuka ganin cewa mace 'yar Najeriya ce ta zama zakara a irin wannan babbar gasa ta duniya.

Yusuf Dukku da Maryam Dan'azumi
Malamin Maryam Dan'azumi tare da ita a Saudiyya. Hoto: Yusuf Muhammad Dukku
Source: Facebook

Ya kuma tuno da wata yarinya 'yar Najeriya mai suna Nafisa Aminu, wadda ta ba Najeriya abin alfahari a shekarar 2025 bayan lashe gasar TeenEagle da aka gudanar a birnin London na kasar Birtaniya.

Nafisa, wadda daliba ce a makarantar NTIC ta jihar Yobe, ta yi nasara ne bayan ta doke mahalarta sama da 20,000 daga kasashe 69.

Tinubu ya taya Maryam murna

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan'azumi murnar lashe gasar Alƙur'ani ta kasa da kasa karo na 46 da aka gudanar a Saudiyya.

Tinubu ya yabawa Maryam kan bajintar da ta nuna, bayan ta doke mahalarta daga kasashe 132 tare da lashe kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira miliyan 120.

Shugaban kasar ya ce nasarar Maryam abin alfahari ga Najeriya, yayin da ya kuma ya yabawa 'yar uwarta Hajara Ibrahim Dan'azumi, wadda ta lashe irin gasar a Jordan a 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng