Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta Sake Kunyata Donald Trump
- Kafofin watsa labaran gwamnatin Iran sun ce tawagar ƙasar da ke taron Majalisar Dinkin Duniya ba ta shirya yin wata tattaunawa da Amurka ba
- Donald Trump ya ce yana sa ran Amurka da Iran za su sake komawa tattaunawa, duk da rashin amincewar Tehran da wasu buƙatun Washington
- Iran ta gabatar da wasu sharuɗɗa bakwai na kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga harkar makamashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Tawagar ƙasar da ke halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) ba ta da wani shirin tattaunawa da Amurka.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana sa ran za a sake komawa tattaunawa tsakanin Washington da Tehran nan ba da jimawa ba.

Source: Getty Images
Iran ta ce ba ta shirya tattaunawa ba

Kara karanta wannan
Amurka ta gode wa Birtaniya da wasu kasashen musulmi 3 kan goyon bayan yaki da Iran
Tashar Arab News ta ce kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito wata majiya da ba a bayyana sunanta ba, wadda ke kusa da tawagar Iran, tana cewa babu wani shirin tattaunawa da Amurka.
“Tawagar Iran da ke New York ba ta da shirin tattaunawa da Amurka,” in ji majiyar.
Trump ya shaida wa kafar yada labarai ta Axios ranar Lahadi cewa yana sa ran tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu za ta sake farawa nan ba da jimawa ba.
Wannan na zuwa kwana guda bayan Trump ya ƙi amincewa da wata shawarar Tehran ta sake buɗe mashigin Hormuz cikin kwanaki bakwai.
Qatar ta shiga tsakani
IRNA ta ce Iran ta riga ta isar da ra’ayoyinta da matsayinta ga Amurka “a bayyane kuma kai tsaye” ta hannun wani mai shiga tsakani daga Qatar.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa tawagar Iran za ta koma Tehran ranar Talata.
A cewar Iran, ta gabatar da sharuɗɗa bakwai da za su taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.
Muhimmancin mashigar Hormuz
Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar makamashi a duniya. Kafin fara yaƙin, kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas da ake safararsu a duniya na ratsa wannan mashiga.
Mashigar ya tsinci kan cikin rikicin da ya fara bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran a watan Fabrairun 2026.
Bayan hare-haren, Tehran ta tsaurara matakan hana zirga-zirga a mashigar, yayin da Washington ta mayar da martani da killace tashoshin jiragen ruwa na Iran.
Iran ta gabatar da wasu sharuɗɗa
A cewar rahotannin, Iran na neman a tsagaita wuta na tsawon kwanaki bakwai a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Buƙatar ta kuma shafi Lebanon, inda Isra’ila ke kai hare-hare akai-akai kan Hezbollah, ƙungiyar da ke da alaƙa da Iran.
Iran ta kuma nemi a cire takunkumin da aka sanya kan kadarorinta da ke ƙasashen waje, a ɗage takunkumin da ya shafi ɓangaren man fetur, tare da kawo ƙarshen killace tashoshin jiragen ruwa da sojojin ruwan Amurka suka yi.
Sai dai Trump ya ƙi amincewa da waɗannan buƙatu ranar Asabar, 26 ga watan Satumban 2026.

Source: Getty Images
Iran ta yi barazana ga Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin ruwa ta IRGC ta Iran ta yi barazanar kai hare-hare idan har aka sake kaddamar da yaki kan kasar.
Rundunar ta yi barazanar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka hari, ciki har da waɗanda ke cikin Tekun Indiya, idan Washington ta ƙaddamar da wani sabon yaƙi da Tehran.
Asali: Legit.ng
