Ba a Gama da Iran ba, Sabon Rikici Ya Barke tsakanin Amurka da Kanada
- Tattaunawar kasuwanci tsakanin Amurka da Kanada ta rushe a bayan dogon zama, lamarin da ya sake kunna rikicin haraji tsakanin kasashen biyu
- Sababbin harajin kashi 50 kan wasu kayayyakin Kanada da darajarsu ta kai dala biliyan 20 sun fara aiki bayan kasashen sun kasa cimma yarjejeniya
- Firaministan Kanada, Mark Carney, ya ce kasarsa za ta mayar da martani kan harajin Amurka da irin matakin da Washington ta dauka domin kare 'yan kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Canada – Tattaunawar kasuwanci tsakanin Amurka da Kanada ta ci tura bayan wani zama da suka yi a ranar Juma'a, lamarin da ya sake jefa makwabtan biyu cikin sabon rikicin kasuwanci.
Rashin cimma yarjejeniyar ya sa sababbbin harajin kashi 50 kan wasu kayayyakin Kanada da darajarsu ta kai dala biliyan 20 suka fara aiki bayan wa'adin da aka sanya.

Kara karanta wannan
Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa gwamnatin Kanada ta bayyana shirinta na mayar da martani daidai da harajin da Amurka ta kakaba domin kare ma'aikata da 'yan kasuwar kasar.
Tattaunawar Amurka da Kanada
Kafin karewar wa'adin, bangarorin biyu sun nuna alamun cewa za su iya cimma yarjejeniya domin kaucewa sabon harajin.
Sai dai Firaministan Kanada, Mark Carney, ya ce kasashen biyu sun kasa cimma matsayar da za ta dace da muradun kasarsa.
A wata sanarwa, Carney ya ce:
"Sakamakon haka, na yanke shawarar dakatar da tattaunawar kasuwanci da Amurka, kuma na umarci masu tattaunawar Kanada su koma Ottawa."
Ya kara da cewa sababbin harajin Amurka sun shafi kayayyakin Kanada da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 20.
Martanin Kanada ga Trump
Carney ya bayyana cewa gwamnatin Kanada za ta mayar da martani kan harajin da Amurka ta kakaba, inda ya ce za su yi hakan daidai da matakin da Washington ta dauka.
"Kanada za ta mayar da martani kan harajin domin kare ma'aikatanmu da 'yan kasuwarmu,"
In ji shi.
A cewar rahoton NBC, Shugaban Amurka Donald Trump da Carney, tare da manyan jami'an kasuwanci daga bangarorin biyu, sun kasance cikin tattaunawa a tsawon makon.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya ba da karin kwanaki uku kafin fara aiwatar da harajin, domin bai wa bangarorin damar kammala yarjejeniyar.
A farkon makon, Trump ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da Kanada, amma ya ce har yanzu ana bukatar kammala wasu takardu kafin tabbatar da ita.
Musulma ta ci zabe a Amurka
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Aisha Wahab ta lashe zaben cike gurbi domin zama mamba a Majalisar Wakilan Amurka, inda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko 'yar asalin Afghanistan da ta shiga majalisar.
Wahab, wacce ke majalisar dattawan jihar California, ta lashe zaben ne bayan wata fafatawa mai zafi tsakanin 'yan jam'iyyar Democrat kan kujerar da tsohon dan majalisa Eric Swalwell ya bari.
Rahotanni sun nuna cewa Aisha ta samu nasara kan Melissa Hernandez, bayan da ta riga ta yi fintinkau a zaben fitar da gwani na musamman da tazarar sama da kuri'a 20.
Asali: Legit.ng
