Latest
Shugabannin kasashen Iran da Rasha na shirin ganawa a Kyrgyzstan yayin da ƙasashen biyu ke ƙarfafa haɗin gwiwar makamashin nukiliya da yarjejeniyar dala biliyan 25.
Tsohon minista, Abubakar Malami ya kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC mai mambobi sama da 600 a Kebbi, inda ya buƙaci haɗin kai da kamfen cikin lumana.
Fadar Shugaban Kasa ta zargi Atiku Abubakar da yin siyasa da batun dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa ya ba ‘yan Najeriya bayanai masu karo da juna.
Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana yadda ta kashe kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur, yana kuma kalubalantar a bincike shi.
’Yan bindiga sun kashe Hakimin Galla, Alhaji Ahmed Yusuf, a Niger bayan ya yi musu gargadi, yayin da Gwamna Bago ya nemi a gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
Atiku Abubakar ya ce zargin sace dala $16bn wayau ne na ɓoye gaskiya kan kuɗin cire tallafin fetur. Ya ƙalubalanci a bincike shi idan ana da huja.
Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da N600bn wajen tallafa wa gidaje masu rauni sama da miliyan 10 cikin shekaru uku, in ji Minista Jin Lai, Bernard Doro.
Sarkin Daura ya nada Folashade Tinubu-Ojo Jakadiyar Kasar Hausa, yayin da Hannatu Musawa ta zama Mairamar Kasar Hausa a wani bikin gargajiya a Katsina.
Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargadi jam’iyyun adawa cewa ba za su iya kayar da Tinubu a 2027 ba sai sun hada kai cikin ingantacciyar kawance.
Masu zafi
Samu kari