Shugaban Kasar Bangladesh Ya Yi Murabus kafin Karewar Wa'adinsa
- Shugaban Bangladesh, Mohammad Shahabuddin, ya yi murabus shekaru kadan bayan kotu ta samu tsohuwar Firaminstan kasar da laifi
- Ana danganta matakin ajiye mukaminsa da rashin jituwar gwamnati da alakar da ake zargin yana da ita da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina
- Kakakin Majalisar Dokoki, Hafiz Uddin Ahmad, zai rike mukamin shugaban kasa na wucin gadi har sai an zabi sabon shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Bangladesh – Shugaban kasar Bangladesh, Mohammad Shahabuddin, ya yi murabus a ranar Juma'a, 24 Yuli, 2026 kusan shekara biyu kafin karewar wa'adinsa na shekaru biyar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake rade-radin akwai wata alaka mai karfi tsakaninsa da tsohuwar Firaminsta, Sheikh Hasina da aka kora bayan zanga-zanga a kasar.

Source: Getty Images
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa murabus din ya zo ne yayin da ake cewa gwamnatin kasar ba ta kara amincewa da ci gaba da zamansa kan mukamin ba.
Shugaban Bangladesh ya yi murabus
Times of India ta kawo labarin cewa rahotanni sun nuna cewa ana kallon Shahabuddin a matsayin na kusa da tsohuwar Firaminista, Sheikh Hasina, wacce aka hambarar daga mulki bayan zanga-zangar dalibai da ta barke a watan Agustan 2024.
Murabus din ya zo ne 'yan kwanaki bayan Hasina, wacce ke zaune a kasar Indiya tun bayan ficewarta daga Bangladesh, ta sanar da shirin komawa gida a watan Disamba domin mika kanta bayan kotun laifukan yaki ta same ta da laifi.
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Bangladesh, Kakakin Majalisar Dokoki, Hafiz Uddin Ahmad, zai kasance shugaban kasa na rikon kwarya har sai an zabi sabon shugaban kasa.
Yadda aka nemi shugaban kasa ya yi murabus
Rahoton ya ce gwamnati ta bukaci Shahabuddin ya sauka daga mukaminsa ne saboda alakarsa da Hasina, musamman bayan sanarwar da ta yi na komawa kasar.
An zabi Shahabuddin ba tare da hamayya ba a shekarar 2023 bayan jam'iyyar Awami League, wacce yanzu aka haramta, ta tsayar da shi takara.

Source: Twitter
Shi ne mutum na karshe da ya rage a manyan mukaman kundin tsarin mulki daga gwamnatin Awami League bayan boren shekarar 2024 da ya tilasta wa Hasina tserewa zuwa Indiya.
Rahotannin kafafen yada labarai na Bangladesh sun ce gwamnati ta kara nuna damuwa bayan rahotannin cewa Shahabuddin ya yi yunkurin sake tuntubar Hasina.
Sai dai wasu manyan 'yan siyasa sun bayyana cewa dalilan murabus dinsa sun fi haka, musamman bayan tsohuwar Firaministar ta bayyana aniyarta ta komawa kasar.
Sojoji sun karbi mulkin Bangladesh
A baya, kun samu labarin cewa yayin da zanga-zanga ta yi kamari a Bangladesh, dubban matasan kasar sun nufi fadar gwamnati da ke Dhaka tare da neman lallai Firaministar kasar ta yi murabus daga ofis.
Sojojin kasar sun bayyana cewa lamarin ya sa dole firaministan kasar, Sheikh Hasina ta ajiye aiki kuma ta gudu zuwa wata kasar yayin da masu zanga-zangar su ka ci gaba da nuna bacin ransu a kan jami'an gwamnati.
Matasa sun tsunduma zanga-zanga kimanin wata guda da ta saboda kin jinin yadda gwamnati ke raba ayyuka, daya daga cikin zang-zanga da ta jawo asarar rayuka da hargitsa kasar na tsawon lokaci
Asali: Legit.ng

