Amaranta Hank: Tsohuwar Shahararriyar Mai fim din Batsa Ta Zama Sanata a Majalisa

Amaranta Hank: Tsohuwar Shahararriyar Mai fim din Batsa Ta Zama Sanata a Majalisa

  • Deyci Alejandra Omaña Ortiz, wadda aka fi sani da Amaranta Hank a harkar fina-finan batsa ta shiga siyasa
  • A makon nan ta zama sanata a Colombia karkashin jam'iyyar Pacto Histórico, za ta wakilci Norte de Santander
  • Ortiz ta samu nasara ne a zaben watan Maris na 2026, za ta yaki zaluncin da ake yi wa tsofaffin abokan aikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Columbia - Tsohuwar mai yin fim din batsa a duniya ta shiga siyasa kuma har ta tsira da babbar kujera ta sanata a majalisar kasar Columbia.

Deyci Alejandra Omana Ortiz da ta fi shahara da sunan Amaranta Hank wajen wasa ta shiga sahun shugabanni masu tsara dokoki a Columbia.

Deyci Alejandra Omaña Ortiz
Sabuwar sanata, Deyci Alejandra Omaña Ortiz da hoton Majalisar Columbia
Source: Getty Images

Deyci Alejandra Omaña Ortiz ta tafi majalisa

A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli 2026 aka rantsar da Deyci Alejandra Omana Ortiz a majalisa kamar yadda muka gani a jaridar New York Times.

Kara karanta wannan

An bayyana yadda Yariman Saudiyya Abdullah bin Fahad ya rasu a otal din Landan

Tsohuwar ‘yar wasar ta yi nasara ne a karkashin jam’iyyar Historic Pact a birnin Bogota.

Kafin zamanta sanata bayan zaben 2026, Deyci Alejandra Omana Ortiz ta kasance ‘yar jarida, daga baya kuma ta koma yin fina-finan batsa.

A shekarar 2017 Deyci Alejandra Omana Ortiz ta shiga harkar wadannan fina-finai lokacin da ta yi bankwana da aikin jarida a Columbia.

Jaridar La Opinión ta ce bayan shekaru biyu rak kuma fitacciyar ‘yar wasar da aka haifa a Satumban 1992 ta sake tsalle ta shigo harkar siyasa.

A watan Maris na 2026 aka zabe ta a yankin Norte de Santander da ke Arewacin Columbia, shiyyar da ke iyaka da kasar Venezuala.

Gwagwarmayar Ortiz a Majalisar Columbia

Yanzu haka ‘yar siyasar ta dage wajen tabbatar da hakkokin masu shirya fina-finan batsa

Ortiz ta yi ikirarin cewa masu aiki a harkokin bidiyon batsa suna bukatar dokokin da za su kare masu hakki, su rika cin moriyar aikinsu.

Ana kukan cewa kamfanoni da dillalai suna zaluntar wadanda suka zabi wannan layi don haka sabuwar sanatar ta tsaya masu a majalisa.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da koma baya, na kusa da El Rufai ya fice daga jam'iyyar a Kaduna

Columbia
Kasar Columbia da jam'iyyar Pacto Historio ta ke haramar barin mulki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lokacin da ta ke yakin neman zabe, ta soki yadda ake shiga hakkokin tsofaffin abokan aikinta.

“Gwamnati ba ta kare wadannan mutane saboda bayanan karya, ra’ayi da munafunci, babu wanda ya tsaya zai gyara harkar.”

Ya kamata masu fim din batsa su rike mukamai?

A sa’ilin da ta ke kamfen, ta yi kaca-kaca da masu cewa tsofaffin masu fitowa a fina-finan batsa bai kamata su nemi mukaman siyasa ba.

Ortiz ta kafa hujja da Ilona Staller wanda ta yi suna wajen wannan harka kafin ta zama ‘yar majalisa a kasar Italiya shekaru 50 da suka wuce.

A cewarta, ta san koken wadannan mutane don haka za ta iya taimakonsu a majalisa.

Sani Danja ya ja layi da bidiyon batsa

Kwanaki an rahoto 'dan fim kuma mawakin Hausa Sani Danja ya bayyana cewa babu adadin kudin da za a biya shi da zai sa ya fito a fim din batsa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta fito gaba gadi tana fada da tikitin Muslim Muslim a 2027

Tauraron ya jaddada cewa kowane mutum yana da iyakokin da bai kamata ya wuce su ba a duk sana'ar da yake yi domin kare mutuncinsa.

Bayan hakan, 'dan wasan ya ja kunnen matasa masu so su yi suna da kada su yarda su zubar da mutuncinsu ko gudanar da dabi'u marasa kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng