Tsaro: Tsohon Daraktan DSS Ta Dura kan Pantami, Ya Faɗi Illar Naɗa Shi Minista
- Tsohon mataimakin daraktan DSS, Dennis Amachree, ya yi magana game da nada Isa Pantami a matsayin minista
- Amachree ya ce yana da wahala a yi zaton jami'an DSS ba su lura da tsofaffin kalaman Pantami ba, amma yiwuwar an yi watsi da rahoton tsaro
- Ya gargadi cewa lamarin ya raunana amincewar jama'a ga yaki da ta'addanci, yana kira a kare shawarar hukumomin tsaro daga tsoma bakin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin daraktan Hukumar DSS, Dennis Amachree ya soki yadda aka nada Isa Pantami minista.
Amachree ya ce nadin nasa a matsayin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ta bayyana gibi a tsaron Najeriya.

Source: Facebook
Amachree ya bayyana haka ne cikin littafinsa mai suna DSS @40: My Journey Behind the Shield, cewar Punch.

Kara karanta wannan
'A guji siyasantar da tsaro': Ɗan APC ya koɗa ministan tsaro kan yaƙi da ta'addanci
An tuna hudubobin Pantami na baya
Ya waiwayi ce-ce-ku-cen da suka taso a 2021 bayan tsoffin hudubobi da kalaman Pantami suka sake bayyana.
Ya ce kalaman da ake zargin Pantami ya taba yi na nuna goyon baya ga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kamar al-Qaeda, Taliban da Boko Haram sun jawo tambayoyi kan yadda ya tsallake tantance tsaro.
A cewarsa, DSS kan gudanar da cikakken bincike kan wadanda ake son nada a manyan mukamai, ta hanyar duba tarihin rayuwarsu, jawabai, karatu, alakoki, ra'ayin siyasa da kuma abubuwan da suka wallafa.
Sai dai ya bayyana cewa aikin DSS shi ne bayar da shawara kawai, yana mai cewa bai tabbatar da abin da rahoton tsaron Pantami ya kunsa ba.
Amma ya ce yana da wahala a yarda cewa jami'an leken asiri ba su lura da tsoffin kalaman Pantami ba, yana mai cewa mai yiwuwa rahoton ya kunshi bayanan da suka shafi lamarin.
Amachree ya ce idan bukatun siyasa, daidaita wakilcin yankuna ko maslahar jam'iyya suka shiga tsakanin, ana iya yin watsi da shawarwarin hukumomin tsaro.
Ya kuma tuna cewa tsohon kakakin kwamitin yada labarai na majalisar dattawa, Ajibola Basiru, ya taba cewa sanatoci ba su samu wani rahoton tsaro mara kyau kan Pantami kafin tabbatar da nadinsa ba.
A cewarsa, hakan na iya nufin ko dai an tace rahoton kafin ya isa majalisar dattawa, ko kuma an yi watsi da bayanan da ke cikinsa saboda dalilan siyasa.
Ya ce wannan lamari ya rage amincewar jama'a da kokarin gwamnati na yaki da Boko Haram da ISWAP, musamman ganin Pantami yana jagorantar ma'aikatar da ke kula da muhimman hanyoyin sadarwa na kasa.
Amachree ya ce darasin da ya kamata a koya shi ne a kara mutunta rahotannin hukumomin tsaro tare da kare su daga tasirin siyasa domin karfafa amincewar jama'a ga cibiyoyin tsaron Najeriya.
Pantami ya kalubalanci yan takara a Gombe
Mun ba ku labarin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana dalilinsa na shiga takarar gwamnan Gombe a 2027, yana mai korafi kan lalacewar lamura.
Pantami ya bayyana cewa babu wata al'umma da ta gyaru da kanta, yana mai cewa sai mutane sun tashi tsaye domin neman sauyi.
Tsohon ministan ya bukaci a shirya muhawara tsakanin dukkan 'yan takara, tare da binciken ayyukansu da ba da damar tonon silili kafin zaben gwamna na 2027.
Asali: Legit.ng
