'Yan Bindiga Sun Birkita Kauyen Sokoto da Harbi, Sun Sace Sama da Mutum 50
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan Sokoto, inda suka sace fiye da mutum 50
- Mazauna garin sun ce maharan sun karɓi N600,000 kafin su saki mutanen, sannan suka umarci al'umma su biya karin N1m cikin kwana biyu
- Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta ce ba ta samu wani rahoto kan harin ba, yayin da mazauna yankin ke neman agajin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Idris Mohammed Gobir, inda suka yi garkuwa da fiye da mutum 50.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun afka wa garin ne tsakanin karfe 10:00 na dare na ranar Litinin zuwa misalin karfe 12:30 na dare na ranar Talata.

Source: Original
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa 'yan ta'addan sun rika harbe-harbe domin firgita mazauna garin kafin su rabu gida biyu suna shiga sassa daban-daban na ƙauyen.
Yadda uka sace mutane a Sokoto
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa rukuni na farko ya kutsa cikin wani gida inda suka tattara kusan mata 30 kafin suka tafi da su cikin daji.
Ya ce rukuni na biyu kuma ya nufi wata makarantar allo inda sama da maza 20, ciki har da tsofaffi da almajirai, ke karatu, sannan suka yi awon gaba da su.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan ya sa jimillar mutanen da aka sace a wuraren ya haura 50.
Mutumin ya kara da cewa kafin maharan su bar garin, sun saki mutum daya daga cikin wadanda suka kama tare da umartarsa ya sanar da hakimi, limamin gari da sauran shugabannin al'umma su zo su same su a daji domin tattaunawa.
Bukatar 'yan bindiga Sokoto
Majiyar ta ce bayan shugabannin al'umma sun gana da maharan, sun bukaci a biya Naira miliyan 1 saboda matan da aka sace, sannan N600,000 kan sauran mutanen.
A cewarsa, bayan dawowar shugabannin, aka yi tattaki daga gida zuwa gida karkashin jagorancin hakimi da limamin gari domin tara N600,000.
Ya ce an kai kudin ga maharan, inda nan take suka saki dukkan mutanen da aka sace. Sai dai ya ce 'yan bindigar sun gargadi al'ummar cewa dole ne su biya ragowar Naira miliyan 1 cikin kwanaki biyu.
Rahoton ya kara da cewa maharan sun sake dawowa garin da misalin karfe 7:00 na yammacin Talata, inda suka bukaci ko dai a ba su wasu mutane ko kuma a ba su N300,000.
An ce cikin gaggawa mazauna garin suka tara kudin suka mika musu, lamarin da ya sa maharan suka dauki lokaci mai tsawo a garin har wasu mazauna suka hada sallar Magariba da Isha kafin su bar yankin.

Source: Twitter
'Yan sanda ba su da masaniya
Mazauna yankin sun roki gwamnati da jami'an tsaro su dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma, suna bayyana cewa mafi yawan mutanen yankin manoma ne.
Trust Radio ya wallafa cewa da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ba ta samu wani rahoto kan harin ba.
A cewarsa, mafi yawan mutanen karkara ba sa kai irin wadannan rahotanni ga 'yan sanda, wanda hakan ke sa rundunar ta kasa samun bayanai cikin lokaci.
Guguwa ta kashe mutane a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane hudu sun rasu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon guguwa da ruwan sama mai karfi a jihar Sokoto.
Hukumar bayar da agaji ta NEMA ta bayyana cewa bala'in ya lalata daruruwan gidaje tare da jefa iyalai da dama cikin halin rashin matsuguni.
Biyo bayan faruwar hadarin, NEMA ta tabbatar da cewa ta fara tantance barnar domin kai daukin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
Asali: Legit.ng


