An Tsinci Gawar Babban Malamin Addini cikin Wani Yanayi a Dakin Otal a Ondo

An Tsinci Gawar Babban Malamin Addini cikin Wani Yanayi a Dakin Otal a Ondo

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani babban malamin cocin C&S, Fasto Omotayo Fajana
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda sun kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin domin taimakawa binciken da suke gudanarwa
  • ‘Yan sanda sun nuna damuwa kan yadda aka kai gawarsa dakin ajiye gawa ba tare da likita ya tabbatar da mutuwarsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani babban limami kuma jigo a Cocin Cherubim da Seraphim (C&S), Omotayo Fajana.

Tun da farko dai an tsinci gawar limamim cocin ne a wani dakin otal da ke Akungba-Akoko a karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je gidan shugaban APC sun sace masa iyalai a Kebbi

Taswirar jihar Ondo.
Taswirar jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta rahoto cewa marigayin mai shekaru 71 ya je Akungba-Akoko ne domin halartar wani taron coci da aka shirya nada shi a matsayin 'Baba Aladura' na Cocin Ogo Orimolade C&S da ke Okerigbo.

‘Yan sanda sun fara bincike

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya bayyana cewa an kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin kuma suna taimakawa jami’an bincike.

Ya ce bayanan farko da aka samu sun jawo tambayoyi kan yadda aka tafiyar da gawar marigayin, musamman yadda aka kai ta dakin ajiye gawa ba tare da samun takardar tabbatar da mutuwa daga likita ba.

A ruwayar Leadership, Jimoh ya ce:

"Rundunar 'yan sanda ta fara cikakken bincike kan mutuwar Omotayo Ezekiel Fajana mai shekaru 71, wanda aka tsinci gawarsa cikin yanayi mai cike da shakku a Akungba-Akoko.”

Yadda aka gano gawar limamin coci

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

A cewarsa, wani ɗan uwan marigayin mai suna Olaseni Sunday Olaoluwa ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ranar Asabar da ta gabata.

Ya bayyana cewa Fajana ya je Akungba-Akoko ne domin wani shirin coci inda aka shirya nada shi a matsayin 'Baba Aladura' na wani bangare na Cocin Cherubim da Seraphim.

Yan sanda.
Jami'an hukumar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Binciken farko ya nuna cewa bayan an gano marigayin ya mutu a cikin dakin otal, wasu mutane da suka hada da jami’an coci da ma’aikatan otal sun dauki gawarsa zuwa wani dakin ajiye gawa da ke Ikare-Akoko.

Sai dai an yi hakan ne ba tare da samun tabbacin mutuwa daga kwararren likita ba, lamarin da ya zama daya daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan sanda ke bincike a kai.

Matashi ya kashe mahaifinsa a Ondo

A wani rahoton, an ji cewa wani matashi mai shekaru 34 mai suna Nsikak Kingsley ya afka wa mahaifinsa tare da yi masa mummunan duka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dukan kawo wuka da yaron ya yi ga mahaifinsa ya yi sanadiyar rasa ransa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Tuni dai aka kama wanda ake zargin kuma yana tsare a hannun dakarun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262