ADC Ta Kalubalanci Tinubu Ya Ziyarci Zamfara bayan Mummunan Hari

ADC Ta Kalubalanci Tinubu Ya Ziyarci Zamfara bayan Mummunan Hari

  • Jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta yi Allah wadai da harin da ya kashe mutane da dama a al'ummar Sauna da ke jihar Zamfara
  • Jam'iyyar ta bukaci gwamnati ta kamo masu laifin da su ka aikata wannan danyen aiki da asarar rayukan bayin Allah, a kuma dauki mataki
  • ADC da ke hamayya da mulkin APC ta roki Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara jihar domin ya tabbatar da wa idanunsa irin kunci da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Jam'iyyar ADC reshen jihar Zamfara ta nuna alhini kan mummunan harin da 'yan ta'adda suka kai wa al'ummar Sauna da ke masarautar Talata Mafara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin Hon. Kabiru Garba Gusau sun bayyana ta'aziyyarsu ga iyalan wadanda suka rasu da daukacin al'ummar karamar hukumar Talata Mafara.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

ADC ta nemi Tinubu ya ba Zamfara kulawa kamar sauran jihohin Najeriya
Tutar jam'iyyar ADC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: ADC Coalition/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

The Guardian ta kawo labarin cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar a jihar, Kwamared Abdulkareem Umar Lihidda, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Gusau.

ADC ta yi takaicin harin Zamfara

Jaridar Daily post ta kawo labarin cewa sanarwar ta bayyana cewa sabon harin ya sake nuna irin matsalar tsaro da ke addabar jihar Zamfara tsawon lokaci.

Jam'iyyar ta ce ta yi Allah wadai da abin da ta kira danyen aiki na rashin tausayi, tare da kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

ADC ta ce akwai bukatar tsare rayuka da dukiyar mutanen Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalar rashin tsaro Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewar sanarwar:

"Muna yin Allah wadai da wannan danyen aiki na rashin imani tare da kira ga dukkan hukumomin tsaro su kara himma wajen kare rayukan jama'a da dawo da kwarin gwiwar al'umma."

ADC ta kuma yi addu'ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka mutu, Ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, tare da ba iyalan mamatan hakurin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Yadda dan takarar gwamna ya kawo ƙarshen rikicin shugabancin ADC a Kaduna

ADC ta kalubalanci Tinubu

Jam'iyyar ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara su dauki matakan gaggawa domin gano wadanda suka aikata harin, a kama su kuma a gurfanar da su gaban kuliya cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce:

"Dole ne adalci ya tabbata, sannan a dauki matakan da za su hana sake kai irin wadannan hare-hare kan al'ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba."

ADC ta nuna damuwa cewa duk da yawaitar hare-hare da matsalolin jin kai a Zamfara, har yanzu Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kai ziyarar aiki jihar ba tun bayan hawansa mulki.

Jam'iyyar ta roki shugaban kasar da ya kai ziyara Zamfara domin jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya duba halin tsaron jihar da idonsa, sannan ya tabbatar wa al'umma cewa gwamnatin tarayya tana tare da su.

An sace dan siyasa a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari har cikin gidan shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara tare da yin garkuwa da shi da wasu daga cikin iyalansa.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta matsa kan binciken yadda ake kashe N25m na tsaro bayan hare hare

Maharan sun kashe jami'an tsaro huɗu da suka haɗa da 'yan sanda biyu da masu sintiri biyu kafin su tsere da shugaban ƙaramar hukumar inda su ka bar jama'a a cikin tashin hankali da jimamin lamarin.

Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun ceto wasu daga cikin 'ya'yan shugaban ƙaramar hukumar yayin da ake bibiyar maharan, amma an tafi da shi kuma zuwa wannan lokaci babu wani bayanin halin da ya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng