Tinubu, Atiku ko Obi: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaben 2027
- Wani fasto daga Najeriya ya yi hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara
- Prophet Elijah Bamidele ya ce zai ga Shugaba Tinubu ya kammala wa'adin mulkinsa na shekaru takwas
- Ya kuma yi hasashen samun sauye-sauyen tattalin arziki, bunkasar ababen more rayuwa da karuwar masu zuba jari daga kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Wani fasto dan Najeriya, Prophet Elijah Bamidele, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu gabanin zaben 2027.
Prophet Elijah Bamidele ya yi hasashen cewa shugaban kasar mai ci zai ci gaba da rike kujerar shugaban kasa a Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta ruwaito cewa Prophet Elijah Bamidele, wanda ke zaune a Legas, ya yi wannan hasashen ne a wani bidiyo da ya yadu sosai a Facebook.
Hasashen Bamidele ya fifita Tinubu
A cikin bidiyon da Legit Hausa ta gani ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026, malamin addinin ya ce hasashensa ya nuna cewa Shugaba Tinubu zai lashe zaben 2027
Bamidele, wanda shi ne shugaban Christ House of Prayer and Deliverance Ministry, ya ce:
“Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Idan masu adalci suna kan mulki, mutane suna murna; amma idan mugaye suka yi mulki, mutane suna makoki.’ Na ga cewa a halin da muke ciki, muna mayar da mutumin kirki ya zama mugun mutum."
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne abu mafi kyau da ya faru da Najeriya a yanzu. A halin yanzu, shi ne mafi kyawun abin da ya faru, kuma da zai iya faruwa da Najeriya.”
Malamin addinin ya ci gaba da cewa:
“Na ga gagarumin sauyi a tattalin arziki. Ababen more rayuwa a ko’ina. Kuma na ga masu zuba jari daga kasashen waje suna tururuwa zuwa Najeriya domin zuba jari. A cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa, batun ‘ba ni da aiki’ zai zama tarihi. Batun rashin tsaro kuma nan ba da dadewa ba zai zama tarihi.”
Ya kara da cewa:
“Na ce ban ga wani a kan kujerar shugaban kasa ba. Har yanzu ina ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Idan kuna fatan jin cewa ya yi barci bai farka ba, kuna bata lokacinku ne, domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kammala shekaru takwas. Na ga ya kammala shekaru takwas.”

Source: Twitter
Tinubu, Atiku da Obi za su fafata a 2027
Za a gudanar da babban zaben Najeriya a ranar 16 ga Janairu, 2027, inda masu kada kuri'a za su zabi shugaban kasa da mataimakinsa, da kuma 'yan majalisar dattawa da ta wakilai. Hakazalika, za a gudanar da zaben gwamnonin jihohi da 'yan majalisun dokokin jihohi daga bisani a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Shugaba mai ci, Bola Tinubu, wanda yana cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar APC, na neman wa'adi na biyu.
Tare da Tinubu, ana kallon tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi a matsayin manyan 'yan takarar da ke kan gaba a tseren neman shugabancin kasar.
Tinubu ya yabi Umahi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Ministan Ayyuka, David Umahi, murnar cika shekara 63 da haihuwa.
Shugaba Bola Tinubu ya yaba da jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa masu ɗorewa a faɗin Najeriya.
Asali: Legit.ng


