Juyin mulki: Yadda Aka Shirya Auka wa Aso Rock, Farmaki Sojoji domin Kifar da Tinubu

Juyin mulki: Yadda Aka Shirya Auka wa Aso Rock, Farmaki Sojoji domin Kifar da Tinubu

  • An fahimci yadda sojoji suka yi tsare-tsare na musamman da nufin hambarar da Bola Tinubu daga kan karaga
  • Bayanai sun nuna yadda ake shirin mamaye Fadar Shugaban Ƙasa da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama
  • Sojojin da ake zargi da shirin tawaye sun rika amfani da kalmomin "noma" da "girbi" don boye shirin juyin mulkin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Bayanai suna ta kara fitowa a game da yadda aka nemi ganin bayan gwamnatin Bola Tinubu ta hanyar juyin mulki a shekarar bara.

Tsarin da sojojin da ake zargi da wannan bakin aikin a 2025 ya bayyana, an fahimci irin yaren da suka rika amfani da shi a lokacin.

Premium Times ta rahoto cewa tabbas an nemi kifar da gwamnati kuma an shirya jami’an da za a kama da manyan sojojin da za a tsare.

Takarda mai dauke da shafuka 7, 400 ta fallasa bayanan sirri, takardun banki da hujjojin da za su jawo a hukunta wadanda aka kama.

Kara karanta wannan

An bankado wani muhimmin sirri na sojojin da ake zargin da kifar da gwamnati

Wannan takarda ta nuna yadda masu juyin mulkin za su yi maganin manyan sojoji kuma a karbe iko da wuraren da jami’an tsaro suke.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da dogarinsa a kasar waje Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kanal Mohammed Ma’aji da M.M. Adamu, Shamsuddeen Bappah da Abdulkarim su ne jami’an sojoji da suka nemi shirya juyun mulkin.

Yaren da masu juyin mulki suka bullo da shi

Illa M. M Adamu wanda shi yanzu yana hannu, sauran sojojin sun shirya ta’adi, suna amfani da salo domin su ga bayan mulkin farar hula.

An gano idan aka yi maganar manoma to ana mufin masu juyin mulki, taki kuwa suna nufin kayan aiki, sai ake kiran ranar aika-aikar da girbi.

Duk inda aka ce abokan aiki kuwa, ana nufin malaman addini da ke yi masu addu’ar nasara.

Yaushe sojoji suka shirya yin juyin mulkin?

Lokacin da aka zaba a fara aika-aikan shi ne 1:00 zuwa 2:00. Idan za a tuna, a irin lokacin nan aka saba gudanar da juyin mulki a tarihin kasar.

Game da rana kuwa, an tsaida kwanaki tsakanin Satumba zuwa 1 ga Okotoba 2026, Manjo Ilyasu Jamilu ya yin karin haske kan wannan.

Kara karanta wannan

Ana murna magana ta lafa, sanatan Amurka yana harin jika wa Tinubu aiki

Manjo Ilyasu Jamilu ya ce masu shirin sun yarda a jinkirta domin ba a gama shirye-shirye ba, kuma ana fama da rashin isassun makamai.

Nauyin da daura wa sojojin tawayen

An tsara kowa yana da aikin da zai yi inda aka bar Usman da dawainiyar kai hari a Aso Rock, har dauke wutar fadar shugaban kasar.

Umoru wanda ma’aikacin kamfanin Julius Berger Nigeria Plc ne da ke aiki a fadar ya nuna masu dauke wuta zai jawo alamar tambaya.

Ibrahim aka shirya zai kula da Hedikwatar tsaro amma daga baya aka bar shi da gidan rediyo sai aka bar Bappah ya tsare sojoji a Neja.

Idan da an yi juyin mulkin, Ibrahim ne zai fitar da sanarwar hambarar da gwamnati a gidan rediyo.

Wanda aka bari da sojojin sama shi ne S.B. Adamu sai aka bar Muhammad Jiddah da dawainiyar tsare gidan Hafun soji, Olufemi Oluyede.

Shi kuma gidan tsohon hafsun tsaro, Janar CG Musa aka bar shi hannun Daniel Yusuf.

Tinubu
Bola Tinubu da ya isa wata kasar ketare da hoton Shugaban Najeriyan tare da mai dakinsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da an yi nasara, Kyaftin Akinwale Yusuf zai shawo kan hedikwatar tsaro a Legas haka kuma an dauki hayar tsohon kanal a aikin.

Kara karanta wannan

Trump ya ji zafin kisan sojojinsa da Iran ta yi, zai karbi gawarwakinsu a wani biki a Amurka

Takardu sun nuna yadda aka shirya amfani da makaman Noel Zuzu a hana jirage sauka ko tashi a filin tashin jiragen sama a Abuja.

Irin wannan aiki aka ba Sunday Felix a filin jirgi na Legas da taimakon wani injiniya.

Ma’aji ya yi bayanin yadda yi tsara-tsare game da makamai da sojoji da za su kifar da gwamnati ta hanyar amfani da motoci kirar Hilux.

Ya za a yi da hafsoshi da rabon mukamai?

Umarnin da wasu suka ce an ba da shi ne su cafke manyan da ake hari ne ba tare da an yi barin wuta ba, sai dai bayanan suna cin karo.

A.D. Dauda ya nuna masu dole sai an cafke ko ma a kashe Janar CG Musa domin idan ba haka ba zai iya kawo wa shirinsu matsala.

Kanal Ma’aji ne aka shirya zai zama shugaban kasa da a ce an yi juyin mulkin kuma nan take zai canza hafsoshin tsaron Najeriya.

Sauran sojojin sun zabi mukaman da suke so idan canjin gwamnati ya yiwu. Jamilu ya nemi a nada shi ADC, Bappah yana son ya rike EFCC.

Kara karanta wannan

Ndume ya musanta zargin shiga tsakani da 'yan bindiga, ya nemi a binciki Kaigama

Wasu sun nuna za su so su zama ministocin tarayya a sabuwar gwamnatin sojojin kasar.

Alkali ya saki malamin da aka kama kan juyin mulki

An ji wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin saki Sheikh Sani Abdulkadir Zariya nan take ba tare da wani sharadi ba.

Kotun, karkashin mai shari'a Peter O. Lifu, ta bayyana tsare malamin ba bisa ka'ida ba da sunan zarginsa da hannu a juyin mulki.

An umarci hukumomin DIA, DSS, EFCC da kuma Bankin Jaiz su biya shi tara tare da cire takunkumin da aka sanya wa asusun bankinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng