'Yan Bindiga Sun Je Gidan Shugaban APC Sun Sace Masa Iyalai a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Je Gidan Shugaban APC Sun Sace Masa Iyalai a Kebbi

  • Wasu rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace matar shugaban APC na Yauri da ɗansa a Jihar Kebbi
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ta dauki matakin fara farautar maharan domin ceto iyalan shugaban
  • A daya bangare kuma, aƙalla mutum takwas ne suka mutu a rikicin manoma da makiyaya da aka yi a yankin Argungu duk a jihar Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari gidan shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Yauri a Jihar Kebbi, Alhaji Yusuf Alhassan, inda suka yi awon gaba da matarsa da ɗansa.

Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Birnin Kebbi ya ce harin ya faru ne a gidan shugaban jam’iyyar da ke unguwar Low-Cost a Yauri.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar babban malamin addini cikin wani yanayi a ɗakin otal a jihar Ondo

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An sace iyalan shugaban APC

Leadership ta wallafa cewa majiyar ta ce maharan sun tafi da matar shugaban jam’iyyar da ɗansa zuwa wani wuri da ba a sani ba a cikin daji.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin bibiyar maharan da ceto waɗanda aka sace.

Ƙoƙarin jin ta bakin shugaban APC domin sanin halin da ake ciki ya ci tura, domin dukkan layukan wayarsa a kashe suke.

An kashe mutum 8 a Kebbi

A wani labarin kuma, aƙalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a garin Gulma da ke ƙaramar hukumar Argungu ta jihar Kebbi.

An ruwaito cewa rikicin ya samo asali ne bayan zargin wani makiyayi bafullatani da kashe wani manomi ta hanyar daba masa wuƙa yayin da yake aiki a gonarsa.

Kisan ya haddasa harin ramuwar gayya daga wasu manoma, waɗanda ake zargin sun kai farmaki matsugunan Fulani da ke kusa, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da kuma ƙara taɓarɓarewar zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya rage albashin ma'aikata suna sa ran za a kara masu

Bayanin 'yan sandan reshen Kebbi

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce jami’an tsaro sun shawo kan rikicin.

Punch ta wallafa cewa ya ce rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana, kuma ya yi sanadin mutuwar mutum takwas.

“Harin ramuwar gayya ne bayan wani makiyayi ya daba wa wani manomi wuƙa har lahira. A halin yanzu komai ya lafa, kuma mutum takwas sun rasa rayukansu,”

In ji kakakin ‘yan sandan.

Suefton 'yan sandan Najeriya
Shugaban 'yan sanda na kasa, Olatunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ceci mutum huɗu da suka jikkata tare da kai su asibiti domin samun kulawa, kafin daga bisani aka sallame su.

An kama 'yan ta'adda a Kaduna

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta yi nasarar kashe wasu 'yan bindiga a Kaduna.

Lamarin ya biyo bayan wani kiran gaggawa da sojojin suka samu ne bayan labarin wani hari da aka yi shirin kai wa, abin da ya jawo musayar wuta.

A wani farmaki na dabam da dakarun Najeriya suka kai Kaduna, sun yi nasarar kama mutane hudu da ake zargi suna da alaka da 'yan bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng