Malamin Musulunci Ya Gargadi Kaduna kan Tikitin Musulmi da Musulmi
- Sheikh Haliru Maraya bai jin dadin yadda Musulmi da Musulmi suke samun tikiti guda a jihar Kaduna
- Tsohon hadimin na Patrick Yakowa da Ramalan Yero yana ganin ba a yi wa Kiristoci adalci a gwamnati
- Tunda Kaduna jiha ce mai mabiya addinai rututu, Maraya ya kawo shawarar a rika tsaida Musulmi da Kirista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Sheikh Haliru Maraya wanda malamin addinin Musulunci ne ya soki yadda aka koma tsaida ‘yan takara a zabe a wasu wurare.
Musamman a Kaduna, tun a zaben 2019 ake tsaida Musulmi da Musulmi takarar gwamna a jam’iyyar APC tare duk da ana da Kiristoci a jihar.

Source: UGC
Halliru Maraya bai tare da Muslim-Muslim
Jaridar Aminiya ta sake rahoto shehin malamin yana sukar wannan tsari, yana ganin babu adalci a tikitin Musulmi da Musulmi da ake yi.
Halliru Maraya ya bukaci jam’iyyun siyasa a jihar Kaduna su saba addinai wajen tsaida ɗan takarar gwamna da kuma mataimakinsa.
Idan aka fito da mutane masu addini daya a tikiti guda a zaben shekarar 2027, malamin yana ganin ba a yi wa sauran jama’a adalci ba.
Sheikh Maraya ya bayyana haka ne da ya zanta da ‘yan jarida a tsakiyar makon nan a garin Kaduna.
Idan musulmi da kirista suka samu wuri a tikiti a zaben gwamna, Maraya yana ganin hakan zai kara wanzar da zaman lafiya a Kaduna.
Jihar Kaduna tana da tarihin rikice-rikice a dalilin sabanin addini tun daga lokacin rigimar Zangon Kataf har zuwa fada kan shari’a.
Tarihin tikitin Musulmi da Musulmi a Kaduna
Malamin ya shiga babin tarihi, ya kawo lokutan da aka rika saba kujerar gwamna da mataimaki tsakanin musulmai da kuma kiristoci.
Musulmi ya fara zama gwamnan Kaduna a 1999 amma a 2010 Patrick Ibrahim Yakowa wanda kirista ne ya mulki jihar kafin ya rasu a 2012.
Shekaru biyu da rabi bayan ya gaji Namadi Sambo, Patrick Yakowa ya rasu a hadarin jirgin sama.
Kafin 2019 akwai irinsu Stephen Shekari, Ambasada Nuhu Bajago da Bernabas Bala Bentex sun rike kujerar mataimakin gwamnan Kaduna.
Gwamna Nasir El-Rufai ya canza wannan tsari a 2019 da ya dauko Hadiza Sabuwa Balarabe a APC.

Source: Facebook
Kiran da Sheikh Halliru Maraya ya yi
A wani ra’ayi da ya sha ban-bam da na wasu malaman Musulunci, shehin darikar ya ce dole shugabanni su zama suna tafiya da kowa.
A cewarsa saboda haka ne kowa ya rika jin cewa yana da matsayi a cikin gwamnati, babu zargin an maida wasu saniyar ware a mulki.
Halliru Maraya ya ce:
“Wannan nuna adalci ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da haɗin kai da kuma sa kowa ya ji yana da muhimmanci a jihar, har ta kai babu wani yanki ko addini da ya ji an yi masa wariya a harkokin gwamnati.”

Kara karanta wannan
'Na shirya a yi tonon silili': Pantami ya bugi kirji kan abubuwan alheri da ya yi
“Hakan zai taimaka ƙwarai wajen haɗa kan al’umma da tabbatar da wakilci na adalci a gwamnati. Addinan Musulunci da Kiristanci duka suna da mabiya masu yawa a jihar, don haka ya kamata a gudanar da al’amura ta hanyar da za ta haɗa kowa domin tare mu samu zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.”
Kiristoci suna neman darektan kamfe a APC
Labari ya zo dazu cewa ganin an tsaida musulmi da musulmi, kiristoci suna barar kujera wajen Bola Tinubu domin su taya APC yakin zabe.
Ƙungiyar Kiristocin Arewa na roƙon shugaban kasa ya sake ba ta kujerar sarkin yakin zabe irin na 2023 domin su nuna karfinsu a siyasa.
A zaben da ya wuce, Simon Bako Lalong ne ya jagoranci harkar yakin neman zaben Tinubu da Kashim Shettima kuma suka yi nasara.
Asali: Legit.ng

