'Ya Kamata Isra'ila Ta Tsaya da Kafarta': Netanyahu kan Taimakon Makamai daga Amurka
- Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan dogaro da kasar ke yi kan Amurka a yake-yaken da ta ke yi
- Netanyahu ya ce ya kamata su rage dogaro da makaman Amurka, tare da ƙarfafa masana’antunsu domin tsayawa da ƙafarsu
- Ya bayyana cewa Isra’ila na ci gaba da fafatawa da Iran da ƙawayenta, yana mai cewa makomar ƙasar za ta dogara ne da ƙarfinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yaba wa Amurka kan gudunmawar da ta ke ba kasar.
Netanyahu ya bayyana cewa ƙasarsa na buƙatar samun ‘yanci daga dogaro da makaman Amurka, tare da bunƙasa masana’antar kera makamai ta cikin gida.

Source: Getty Images
Yayin wata ganawa da jami’an rundunar ajiya a yankin Gush Etzion da ke Yammacin Kogin Jordan, Netanyahu ya ce yana matuƙar godiya ga goyon bayan Amurka, cewar Al Jazeera.
Netanyahu ya fadi abin Isra'ila ke bukata
Netanyahu ya ƙara da cewa dole ne Isra’ila ta rika ƙera makaman da kanta domin tabbatar da tsaron ƙasa da kuma fuskantar barazanar da take gani.
Ya ce:
“Ina matuƙar yaba wa tallafin da muka samu daga abokanmu na Amurka tsawon shekaru.
"Amma yau ina cewa muna buƙatar tsarin kera makamai namu.”
A cewarsa, Isra’ila na fafatawa da Iran da ƙungiyoyin da ke goyon bayanta, kuma ta yi musu mummunar illa, duk da cewa rikicin bai ƙare ba.
Ya ce makomar Isra’ila a shekaru 30 masu zuwa za ta dogara ne da irin ƙarfin da ƙasar ta gina a yau da kuma matakan tsaro.
Firaministan ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin samun ƙarin ƙarfi, haɓaka fasahohi, da kuma horar da sababbin shugabannin rundunonin soji masu ƙwarewa.
Ya ce burinsa shi ne Isra’ila ta mallaki cikakkiyar damar kera makamai da kanta domin rage dogaro da tallafin ƙasashen waje.

Source: Facebook
Alwashin da Netanyahu ya sha kan Amurka
Netanyahu ya sha alwashin kawo ƙarshen taimakon sojin Amurka ga Isra’ila a cikin shekaru 10 masu zuwa, yana mai neman sabuwar hanya, cewar Times of Israel.
Kalaman nasa sun zo ne yayin da ake nuna damuwa a Isra’ila kan yiwuwar Amurka ta ƙara takaita wasu matakan soji yayin tattaunawa da Iran.
Ya ce:
“Muna buƙatar kuɓuta daga dogaro, mu ci gaba da kara ƙarfi, mu ƙara amfani da fasaha, kuma mu horar da ƙarin shugabanni.”
A makon da ya gabata, Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce kusan kashi biyu bisa uku na makaman kariyar da suka taimaka wa Isra’ila sun fito ne daga Amurka.
Isra'ila ta yi barazana ga Siriya
An ji cewa Ministan Benjamin Netanyahu, Amichai Chikli ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta iya kai wa Siriya hari a wani lokaci mai zuwa komai dadewa.
Chikli ya zargi wasu kasashe kamar Qatar,Turkiyya da Pakistan da taka rawa wajen tsara yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran.
Kalaman ministan sun zo ne bayan rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin da suka yi a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


