Latest
Majalisar Koli ta Shari’a ta nuna damuwarta kan ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai kiran a bi tsarin shari’a na adalci.
ADC ta zargi Atiku da amfani da sunan jam’iyya ba bisa ka’ida ba, tare da yin Allah-wadai da ƙoƙarin haɗa ta da wasu jam’iyyu gabanin zaɓen 2027.
Mataimakin Shugaban NDC na Arewa maso Yamma, Rabiu Bakinzuwo, ya janye goyon bayan Peter Obi ya koma bayan Atiku Abubakar saboda alkawarin maida tallafin fetur.
INEC ta musanta wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa INEC na daukar ma’aikatan wucin gadi tare da horas da su gabanin babban zaben 2027.
EFCC ta ce ta kwato N1.23 tiriliyan da miliyoyin daloli, fam da euro daga kadarori da kuɗaɗen da ake dangantawa da laifukan tattalin arziki tsakanin 2023 da 2026.
Peter Obi ya ce rashin shugabanci nagari da halayen ’yan siyasa ne ke jefa Najeriya cikin matsaloli, yana roƙon ’yan ƙasa su yi wa shugabanni addu’a.
Sanarwar masarauta ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Zurmi da ke jihar Zamfara, Bello Suleiman, ya riga mu gidan gaskiya bayan shekara biyar a kan mulki.
Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya yi alkawarin goyon bayan duk wani dan takarar ’yan adawa da zai fito daga tsarin hadaka a zaben 2027.
Peter Obi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan batutuwan da suka shafi tarihinsa, musamman karatunsa da aka jima ana magana.
Masu zafi
Samu kari