Karuwai Sun Shiga Matsala saboda Karancin Maganin HIV

Karuwai Sun Shiga Matsala saboda Karancin Maganin HIV

  • Karuwai da sauran ’yan Najeriya da suka cancanci kariyar HIV sun fara neman allurar Lenacapavir da ake yi sau biyu a shekara
  • Rahotanni sun nuna cewa karuwar bukatar allurar ta sa kayayyakin sun kare a wasu jihohin da ke cikin shirin gwajin gwamnatin tarayya
  • Jihohin Benue, Kwara, Gombe da Cross River na daga cikin wuraren da aka samu karancin allurar watanni kadan bayan fara amfani da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Karuwai da sauran mutanen da suka cancanci kariya daga kamuwa da HIV na kara neman allurar Lenacapavir, wadda ake yi sau daya duk bayan wata shida.

Rahotanni sun nuna cewa karuwar bukatar allurar ta jawo karancin ta a wasu jihohin da ke cikin shirin gwajin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur

Wasu karuwai a Najeriya
Wasu mata masu zaman kansu a jihar Edo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda allurar ke karewa

Punch ta wallafa cewa a jihohin Benue, Kwara, Gombe da Cross River sun fuskanci karancin allurar tun bayan fara rabawa a wuraren da aka zaba domin gudanar da shirin.

A Benue, Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jin Dadin Jama’a, Dakta Paul Ogwuche, ya ce sama da mutane 2,000 da ba su da HIV sun karbi allurar tun lokacin da aka fara amfani da ita a watan Mayu 2026.

Ya ce rabon farko da jihar ta samu ya kare a cibiyoyin lafiya da ke gudanar da shirin, amma ana kokarin samar da karin allurai.

Ogwuche ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka karbi allurar sun samu wasu kananan illoli, wadanda jami’an lafiya ke ci gaba da sanya ido a kansu.

Karuwai na bukatar allurar

A Cross River, bukatar allurar ta karu musamman tsakanin karuwai, wadanda suka bayyana cewa allurar ta fi dacewa da su saboda ba sai sun rika shan maganin kariyar HIV na yau da kullum ba.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matar aure kan yanayin yadda saurayinta ya mutu a ɗakin Otal

Ma’aikatan lafiya a wasu cibiyoyin lafiya da ke Calabar sun ce kason farko da jihar ta samu ya fara karewa tun karshen watan Agusta.

Sun ce a farko mutane ba su nuna sha’awa sosai ba saboda rashin wayar da kan jama’a da kuma kyamar da ake yi kan batun HIV, amma bukatar allurar ta karu a cikin wata biyu da suka gabata.

A Calabar, ma’aikatan lafiya sun tabbatar da karancin allurar, yayin da suke jiran karin kayayyakin.

Taswirar Abuja a Najeriya
Taswirar Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Halin da ake ciki a Legas

Yayin da wasu jihohi ke fama da karancin allurar, jami’an lafiya a Lagos sun ce jihar tana da isasshen adadi amma mutane kalilan ne ke zuwa domin karbarta.

Wani jami’in Sashen HIV na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Lagos ya ce suna bukatar karin wayar da kan jama’a domin mutanen da suka cancanta su amfana da allurar.

An raba allurai 11,520 a jihohi

Lenacapavir magani ne da kamfanin Gilead Sciences ya samar domin kariya daga kamuwa da HIV, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da shi a matsayin wata hanyar kariya daga cutar.

Kara karanta wannan

Barayin waya sun shiga gida sun kashe uwa mai yara 5 da wuka a Gombe

Ana yin allurar sau daya duk bayan watanni shida, wanda ya bai wa mutanen da suka cancanta wata hanya ta kariya maimakon shan kwayoyin magani a kullum.

Gwamnatin tarayya ta karbi allurai 11,520 a ranar 19 ga Maris, 2026, sannan ta raba su bayan kwanaki biyar ga wurare 10 da aka zaba domin gwajin shirin.

Jihohin Benue, Kwara, Akwa Ibom, Cross River, Gombe, Anambra, Ebonyi, Kano, Lagos da Abuja ne suka samu allurar.

An kashe wata mata a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata mata mai ’ya’ya biyar ta rasu a Gombe bayan wasu da ake zargin masu kwacen waya sun caka mata wuƙa a cikin gidanta da dare.

’Yan uwanta sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a, inda suka ce an kai mata harin ne a lokacin da take cikin gidanta.

An shirya gudanar da jana’izarta a Masallacin Juma’a na Bolari da ke Gombe da misalin ƙarfe 11:00 na safe, yayin da ake jiran karin bayani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng