Shugaban Jam’iyyar NDC a Arewa Ya Rabu da Obi, Ya Koma Tallar Takarar Atiku
- Muhammadu Rabiu Bakinzuwo ya ayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar saboda alkawarin maido tallafin mai
- ‘Dan siyasar ya soki Peter Obi saboda goyon bayan cire tallafin man fetur, wanda a cewarsa ya sa jama’a cikin kunci
- Idan ta kama, Alhaji Bakinzuwo yana iya sauya-sheka daga jam’iyyarsa ta NDC tun da ya ce Kur’ani ba ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Mataimakin shugaban NDC na kasa na shiyyar Arewa maso yamma, Muhammadu Rabiu Bakinzuwo ya bijire wa jam’iyyarsa.
Alhaji Muhammadu Rabiu Bakinzuwo ya bayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar wanda yake takarar shugaban kasa a wata jam’iyya dabam.

Source: Twitter
Muhammadu Bakinzuwo ya kunyata jam'iyyar NDC
Shugaban jam’iyyar na jihohin Arewa maso yamma yana tare da ‘dan takaran ADC saboda alkawarin maido tallafin man fetur in ji Daily Nigerian.
Muhammadu Bakinzuwo ya ce wannan magana ta karya farashin fetur ta jawo mutane sun fara goyon bayan Atiku domin samun saukin rayuwa.
Ko da akwai siyasa a lamarin, ‘dan adawar ya ce mutane sun soma kyautata wa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya zato a zaben 2027.
Peter Obi ya sha suka daga shugaban NDC
Bai tsaya nan ba, Bakinzuwo ya soki Mista Peter Obi wanda yake takara a jam’iyyar tasu, ya kuma yi barazanar zai iya barin jam’iyyar NDC.
‘Dan siyasar ya yi kaca-kaca da ‘dan takaran shugaban kasar na NDC ne saboda yana goyon bayan janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
Tunda jam’iyyar NDC ba Kur’ani ba ce, ya nuna yiwuwar ya sauya-sheka ko ya bar tallar Atiku idan ya ga wani ‘dan takaran da ya fi shi a badi.
Ya yi wannan magana ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Hantsi TV, ya zargi Obi da kin damuwa da halin da talakawa suke ciki a Najeriya.
Bakinzuwo ya manta da NDC, ya yabi Atiku
Bakinzuwo yake cewa idan dai mutum ba yana ciki mugaye kuma marasa imani ba, dole ya jinjina wa alkawarin da Atiku Abubakar ya dauka.
Shugaban na NDC ya dauki zafi, yana cewa idan har munafukai ba za su jinjina wa ‘dan takaran ADC na zaben 2027 ba, shi dole zai yabe sa.
Ko da Atiku karya yake sharba wa mutane, Bakinzuwo ya ce ana jin dadin zakin-bakin kuma ya ba shi shawarar ya cigaba da irin wannan salo.
Har da cewa Ubangiji zai biya tsohon mataimakin shugaban kasar saboda wannan alwashi.
Shugaban NDC ya yi tir da mulkin Tinubu
Jagoran na ADC ya zargi Bola Tinubu da jefa al’umma cikin kunshi a sanadiyyar janye tallafin mai, lafta haraji ga kuma karin kudin lantarki.
Ya kuma yi tir da karin kudin yin waya da farashin gas na girki, ya ce da za a iya da sai an sa harajin shan iska amma duk da haka ana tallar APC.

Source: Getty Images
Alkawarin maido tallafin mai Atiku ya yi
Idan aka zabe shi a 2027, an ji Atiku Abubakar ya sha alwashin dawo da tallafin man fetur, tsarin da Bola Tinubu ya yi watsi da shi da ya hau mulki.
Masu neman dawo da tallafin man fetur sun kunshi Atiku Abubakar mai rike da tutar ADC da kuma Yele Sowore da ya dade yana takara a AAC.
Gbenga Olawepo-Hashim ya ce babu dan Najeriya da zai sayi litar fetur sama da N610 a karkashin gwamnatin Accord idan dai suka ci zabe a 2027.
Asali: Legit.ng

