Babbar Nasara: Sojoji Sun Kashe Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda 2 a Katsina

Babbar Nasara: Sojoji Sun Kashe Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda 2 a Katsina

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ’yan ta’adda ta Kachalla Muhammadu Filani
  • Kachalla Muhammadu Filani ya tsere daga musayar wutar da raunukan harbi, yayin da sojoji ke ci gaba da nemansa
  • Al’ummomin Matazu da makwabta sun ce ayyukan kungiyar sun haddasa sace-sace, kisa, satar dabbobi da hana manoma zuwa gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation Fansan Yamma ta kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ’yan ta’adda da ke ƙarƙashin jagorancin fitaccen ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu Filani.

An kashe kwamandojin biyu, Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, da Umar Bocho, yayin wani samame da sojoji suka gudanar a kusa da ƙauyen Kogo da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

Sojoji sun kashe kwamandojin 'yan ta'adda a Katsina
Dakarun sojojin Najeirya a bakin fagen daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, yayin wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri, kamar yadda daraktan yada labarai na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal, Aliyu Danja ya bayyana cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Mamiyo shi ne na biyu a kungiyar

Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce dakarun Sector 2 sun yi arangama da ’yan ta’addan a wata maboyarsu. Ya ce sojojin sun yi musu ruwan wuta bayan da suka gamu da turjiya, lamarin da ya kai ga kashe Mamiyo da Bocho.

Aliyu Danja ya bayyana Mamiyo a matsayin fitaccen mai safarar makamai kuma mataimakin Muhammadu Filani na biyu.

Ya ce Umar Bocho ma yana daga cikin manyan ’yan kungiyar da ke da muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukanta.

Muhammadu Filani ya tsere da raunuka

A cewar sojojin, Kachalla Muhammadu Filani ya tsere daga wurin arangamar bayan ya samu raunukan harbi.

Dakarun sun ci gaba da bincike a yankin domin gano inda jagoran ’yan ta’addan yake da kuma cafke sauran mambobin kungiyar.

Rundunar ta bayyana kashe kwamandojin biyu a matsayin babban rashi ga kungiyar, tana mai cewa hakan zai rage karfinta na gudanar da hare-hare da sauran ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan ta'adda a Katsina, an kashe babban kwamanda

’Yan ta’addan sun addabi al’ummomi da dama

Mazauna yankunan da ke kusa da wurin sun bayyana cewa ayyukan kungiyar sun shafi Ƙananan Hukumomin Matazu, Musawa, Dutsinma, Kankia da Kusada.

Sun ce an dade ana samun rahotannin sace mutane, kashe-kashe, satar dabbobi da kuma hana manoma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Wani mazaunin yankin ya ce samamen sojojin ya kawo ɗan sauƙi ga al’ummomin da suka shafe lokaci suna rayuwa cikin fargaba.

Ya ce manoma musamman sun sha fama da rashin iya zuwa gonakinsu saboda tsoron hare-haren ’yan ta’adda.

An bukaci sojoji su ci gaba da matsa lamba

Wani shugaban al’umma ya yaba da aikin sojojin, amma ya bukace su da su ci gaba da matsa lamba kan ’yan kungiyar.

Ya ce hakan zai hana sauran mambobin kungiyar sake haɗuwa da karfafa kansu domin ci gaba da kai hare-hare.

Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna Matazu da sauran yankunan da ke makwabtaka da ita, da ma ma’aikatan lafiya, da su sanar da jami’an tsaro duk wani mutum da ake zargi ya samu raunukan harbi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano, an sace babban mai rike da sarauta da kashe mutane

Sojojin sun ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan neman Muhammadu Filani da sauran ’yan kungiyar, tare da share sauran barazanar tsaro daga yankin.

Sojoji sun hallaka kwamandojin 'yan ta'adda a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kara zafafa kai hare-hare yaki kan ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a jihohin Katsina da Zamfara.

Hare-haren sama sun kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da wadanda suka tsira suka bar baburansu suka tsere zuwa dazuzzukan da ke kewaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng