2027: Gwamna Ya Yi Alkawarin Gyara Najeriya cikin Shekaru 4 idan Ya Zama Shugaban Kasa

2027: Gwamna Ya Yi Alkawarin Gyara Najeriya cikin Shekaru 4 idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin sake fasalin Najeriya cikin shekaru hudu idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027
  • Dan takarar shugaban kasa na APM ya ce zai mayar da hankali kan tsaro, ilimi, tattalin arziki da yanayin siyasa da zamantakewa
  • Makinde ya ce al’ummar Najeriya ne za su yanke hukuncin zaben 2027, ba attajirai ko masu hasashen zabe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa na APM kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi alkawarin sake fasalin Najeriya cikin shekaru hudu idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.

Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Lafia, Jihar Nasarawa, yayin taron tuntuba da jama’a na yankin Arewa ta Tsakiya da ya shirya a matsayin wani bangare na yakin neman zabensa.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Injiniy Seyi Makinde a wurin kaddamar da kamfen APM a Abuja Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Ya bayyana kansa a matsayin wanda zai sake ceto kasar nan, inda ya tabbatar da cewa idan aka zabe shi, zai iya sake gina kasar cikin shekaru hudu, kamar yadda Daily Trust.

“Ni mai ceto ne, kun shirya aikin ceto? Tare za mu hadu mu ceto wannan kasa,” in ji shi.

Makinde ya shirya gyara Najeriya

Makinde ya ce ajandar sake fasalin Najeriya za ta shafi tsaro, ilimi, tattalin arziki da yanayin siyasa da zamantakewa, kuma za a iya kammala ta cikin wa’adi guda na shekaru hudu.

“Ku saurare ni sosai, za nu iya gyara kasar nan cikin shekaru hudu., mun taba samun wanda ya kasance shugaban kasa na tsawon watanni 10, kuma ya iya kawo karshen mulkin soja tare da shimfida dimokuradiyyar da muke morewa a yanzu,” in ji shi.

A cewarsa, idan ya zama shugaban kasa daga ranar 29 ga Mayu, 2027, zai kafa gwamnatin hadin kan kasa domin samun ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Naja da sauran mata 10 da suka samu shiga kwamitin yakin neman zaben Atiku

“Za mu iya sake fasalin wannan kasa. Mu sake fasali tare da samar wa Najeriya da sabon tsarin tsaro. Mu sake fasali tare da samar wa Najeriya sabuwar hanya a bangaren ilimi, mu sake fasalin tattalin arzikinmu.

- Gwamna Seyi Maki kinde.

Makinde ya yabawa gwamnatin Nasarawa

Makinde ya gode wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, da gwamnatin jihar da al’ummar jihar bisa karbar tawagarsa tun bayan isowarsu, yana mai cewa ba su gudanar da siyasa cikin kiyayya ba.

Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da tambarin jam'iyyar APM Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Ya ce ya saurari kungiyoyin mata, ciki har da matan da ke aikin noma, ’yan kasuwar mata, mata masu nakasa da zawarawa, inda ya tabbatar musu da cewa za a samar da shirye-shirye na musamman domin su.

Gwamnan Oyo ya ce al’ummar Najeriya ne za su yanke hukuncin zaben 2027, ba masana harkokin siyasa ko attajirai ba.

Makinde da APM sun kai kara kotu

Kun ji cewa jam’iyyar APM da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Gwamnan Oyo Seyi Makinde , sun kai Gwamnan Abia Alex Otti kotu.

Makinde da APM sun kai kara kotu kan kuɗi har N200m da ake buƙata daga masu takarar shugaban ƙasa domin sanya allunan talla da yaƙin neman zaɓe a jihar Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262