Ana Zargin Tinubu Ya Aikata Abin da Bai Dace ba, Ya Saba Wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

Ana Zargin Tinubu Ya Aikata Abin da Bai Dace ba, Ya Saba Wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

  • Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da karya dokar Kundin Tsarin Mulkin Najeriya
  • Dalung ya ce Kundin Tsarin Mulki bai amince da kalmar “hutu na aiki” ba, yana mai cewa ya tanadi abin da ya kamata shugaban ƙasa ya yi yayin tafiya hutu
  • Ya kuma tambayi dalilin da ya sa Majalisar Dokoki ta Kasa ba ta yi amfani da tanadin Sashe na 145(2) ba bayan kwanaki 21

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da keta tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dalung ya ce Tinubu ya akarya doka ne ta hanyar tafiya hutu ba tare da mika ragamar mulki ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ba yayin ba.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 7 sun hada kai domin kifar da Tinubu a 2027

Dalung.
Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Solomon Dalung, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dalung ya bayyana hakan ne a shirin News Hour na Daily Trust ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan tsawaita hutun Shugaba Tinubu a kasar waje.

Dalung ya zargi Shugaba Tinubu

Da yake magana kan lamarin, Dalung ya ce Kundin Tsarin Mulki bai amince da kalmar “hutun aiki” ba, yana mai dagewa cewa tanadin da ya dace ya bayyana abin da ya kamata ya faru idan shugaban ƙasa ya tafi hutu.

“Shugaban Najeriya ya tafi hutu, an sanar da cewa zai tafi hutu na aiki. Haka kuma, kalmar hutu na aiki ba ta dace da abin da Kundin Tsarin Mulkinmu ya sani ba.
“Babu wani abu da ake kira hutu na aiki ko hutun aiki. Kundin Tsarin Mulki bai amince da hakan ba. Kafafen yaɗa labarai ko manema labarai ba za su iya gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da sanarwar manema labarai ba.
“Abin da muke magana a kai shi ne ko shugaban ƙasa ya bi Kundin Tsarin Mulki ko ya saba ma shi, kuma a ra’ayina, ya yi hakan."

Kara karanta wannan

Magu: Bukola Saraki ya samu abin magana da kotu ta wanke shi a sabaninsa da Buhari

- Solomon Dalung.

Dalilin zargin Tinubu da karya doka

Dalung ya ce batun ba wai ko Tinubu ya ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati daga ketare ba ne, illa ko an bi tsarin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada game da hutun shugaban ƙasa

A rahoton Vanguard, Dalung ya ce:

“Batun a nan ba wai rashin shugaban ƙasa ya shafi wani abu ba ne, batu ne na Kundin Tsarin Mulki wanda Sashe na 145, ƙaramin sashe na 1, ya yi bayani a kansa.
“Dokar a bayyane take, idan shugaban ƙasa ya tafi hutu. Ko hutun rana ɗaya ne, ko mintuna biyar ne, Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa ba za a bar wani gibi ba ko kaɗan.
“Ba batun gudanar da aikin gwamnati ba ne, dole ne ya mika ragamar aikinsa ga mataimakinsa, kuma kalmar da aka yi amfani da ita a nan ita ce ‘shall’."
Dalung.
Tsohon ministan harkokin matasa da wasanni, Solomon Dalung Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

Tsohon ministan ya kuma tambayi dalilin da ya sa Majalisar Dokoki ta Kasa ba ta yi amfani da Sashe na 145(2) ba, wanda ya tanadi matakin da za a ɗauka idan shugaban ƙasa ya kasa aika sanarwar da ake bukata cikin kwanaki 21.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

Shin Tinubu na shi da lafiya ne?

Kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya duk da rashin ganinsa a Abuja da taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Fadar ta ce Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya, yana kuma ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yayin da yake hutun shekara-shekara a ƙasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262