Wani Kaya Sai Amale: Yadda EFCC Ta Kwato N1.3trn a Hannun Barayi
- Hukumar EFCC ta bayyana adadin makudan kudaden da ta kwato a tsakanin watan Oktoba 2023 da Yuni 2026
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce N397.26 biliyan daga cikin kuɗin naira an kwato su ne kai tsaye domin gwamnatin tarayya
- Hukumar ta ce N836.34 biliyan da aka kwato sun kasance kuɗaɗen da aka dawo da su a madadin ma’aikatu daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta bayyana adadin makudan kudaden da ta kwato cikin shekara uku.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kwato N1.23trn da wasu makudan kuɗaɗe na wasu ƙasashe cikin kusan shekaru uku.

Source: Facebook
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 yayin da yake ganawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida a Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.
Olukoyede ya ce tsakanin ranar 1 ga Oktoba, 2023 da 30 ga Yuni, 2026, hukumar ta samu nasarar kwato kuɗaɗe da kadarori da aka gano suna da alaƙa da laifuffukan kuɗi.
Adadin kuɗin da aka kwato
A cewar shugaban EFCC, jimillar kuɗin da aka kwato a wannan lokacin sun haɗa da:
- N1,233,612,040,411.11
- $684,478,457.32
- £373,905.78
- €9,343,803.66
Ya ce hukumar ta kuma samu wasu kuɗaɗe a wasu nau’ukan kuɗin ƙasashen waje.
Gwamnatin tarayya ta samu N397.26bn kai tsaye
Olukoyede ya bayyana cewa daga cikin kuɗin naira da hukumar ta kwato, N397.26bn, wato kusan kashi 33 cikin 100, an dawo da su ne kai tsaye domin gwamnatin tarayya.
Ya ce sauran N836.34bn, wanda ya kai kusan kashi 67 cikin 100, an kwato su ne a madadin ma’aikatu daban-daban na gwamnatin tarayya.
“Daga cikin kuɗin naira, kusan N397.26bn, wanda ya kai kashi 33 cikin 100, sun kasance kuɗaɗen da aka kwato kai tsaye domin gwamnatin tarayya.”

Kara karanta wannan
"Gwamnatinmu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC
“Yayin da N836.34bn, wanda ya kai kashi 67 cikin 100, suka kasance kuɗaɗen da aka kwato a madadin ma’aikatu.” In ji shi
EFCC ta jaddada muhimmancin kwato kadarori
Shugaban hukumar ya ce kwato kadarori da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar aikata laifuffukan tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da EFCC ke mayar da hankali a kai.
Ya ce wannan mataki na taimakawa wajen yaƙi da laifuffukan tattalin arziki da na kuɗi, tare da kare dukiyar gwamnati daga ɓarna da wawurewa.
Olukoyede ya kuma bayyana kwato kadarori a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan ayyukan hukumar tun bayan da ya karɓi shugabancinta.

Source: Twitter
EFCC za ta daukaka kara kan Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya yi magana kan kwace kadarorin Abubakar Malami.
Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya yi watsi da buƙatarta ta kwace kadarori tara da ake dangantawa da tsohon Antoni-Janar din na Tarayya.
Asali: Legit.ng
