Yan Bindiga Sun Bi Dare, Sun Kama tare da Kashe Sakataren Harkokin Lafiya a Katsina
- Yan bindiga sun yi garkuwa da Sakataren Lafiya na Karamar Hukumar Malumfashi, Sa’adu Dantutture, tare da kashe shi a garinsu na Dantutture
- Rahoto ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe jami'in gwamnatin ne yayin wani hari da suka kai kauyen a daren Laraba
- An binne marigayin a garinsu yayin da iyalansa, abokan aikinsa, abokansa da mazauna yankin suka shiga jimami da addu’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Yan bindiga sun sace Sakataren Lafiya na Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, Sa’adu Dantutture, tare da kashe shi a mahaifarsa da ke Karamar Hukumar Kafur.
Dantutture, wanda a baya ya kasance Daraktan Kula da Lafiya a Matakin Farko na Karamar Hukumar Funtua, an yi garkuwa da shi ne jim kadan bayan ya koma garin, yayin wani hari da aka kai a daren Laraba.

Kara karanta wannan
Duk da sulhun da gwamna ya yi, Fulani sun bi dare sun yi wa mutane kisan rashin imani

Source: Original
Yan bindiga sun kashe jami'in gwamnati
Wani ganau, Kabir Ado Mai Unguwa, ya ce shaida wa Daily Trust cewa maharan sun shiga garin da misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka wawashe kayan wasu shaguna sannan suka tafi da Dantutture.
Ya ce maharan sun kashe shi ne yayin da suke ƙoƙarin barin garin.
“Da farko sun yi garkuwa da shi suka tafi da shi bayan sun wawashe kayan wasu daga cikin shagunanmu. Amma yayin da suke barin ƙauyen, sai suka kashe shi,” in ji shi.
An kashe wasu daga cikin yan bindigan
Mai Unguwa ya ce dakarun rundunar sojojin Najeriya ta 17 Brigade, tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai, sun fafata da maharan.
Rahotanni sun ce an kashe mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne, yayin da wani ya tsere bayan ya bar makaminsa.
An binne Dantutture a garinsu cikin kuka da addu’o’in ‘yan uwa, abokan aiki, abokai da mazauna yankin.

Kara karanta wannan
Kaico: Abin da ya faru wanda ya kai ga kashe babban malamin jami'ar ABU, ya ba da wasiyya
Matar marigayin, Fatima Sa’adu, ta bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa al’ummarsa hidima.
Ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara kaimi wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro tare da kare rayukan jama’a.
Ciyaman din Funtua ya yi ta'aziyya
Dantutture ya yi aiki a matsayin Daraktan Kula da Lafiya a Matakin Farko na Karamar Hukumar Funtua kafin daga bisani ya zama Sakataren Lafiya na Karamar Hukumar Malumfashi.

Source: Twitter
Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Abdulmutallib Sulaiman Goya, wanda ya ziyarci iyalan marigayin, ya bayyana shi a matsayin ma’aikacin gwamnati mai gaskiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa mutane hidima.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce zai tabbatar da rahoton kissn jami'in lafiyan kafin ya fitar da sanarwa a hukumance.
An kashe yan bindiga 18 a Katsina
Kun ji cewa jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 18 a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
Jami’an tsaro sun ƙwato bindigar G3 guda ɗaya, bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 14, babura uku, shanu biyu da tumaki 94 da ake zargin ‘yan ta’addan sun sace.
Asali: Legit.ng