Najeriya Ta Tafka Rashi, Allah Ya Yi wa Mai Martaba Sarkin Zurmi Rasuwa

Najeriya Ta Tafka Rashi, Allah Ya Yi wa Mai Martaba Sarkin Zurmi Rasuwa

  • Rahotanni sun nuna cewa Mai Martaba Sarkin Zurmi da ke jihar Zamfara, Bello Suleiman, ya riga mu gidan gaskiya bayan shekara biyar a kan mulki
  • Mai martaban ya rasu ne a ranar Litinin 31 ga watan Agusta, 2027 da tsakar rana a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gusau
  • Zurmi, wadda ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar tare da raba iyaka da jihar Katsina, ita ce gari na biyu mafi yawan al’umma a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zurmi, Zamfara - Mai martaba Sarkin Zurmi da ke jihar Zamfara a shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, Bello Suleiman, ya riga mu gidan gaskiya.

A wata sanarwa da fadar masarautar ta fitar ta bayyana cewa mai martabar ya rasu ne da yammacin yau Litinin, 31 ga watan Sgustan 2027 a asibiti gwamnatin tarayya (FMC), da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yadda ake ciki a kasar Nijar da sojoji suka yi yunkurin yi wa Tchian juyin mulki

Sarkin Zurmi.
Mai martaba Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Suleiman Hoto: Masarautar Gusau
Source: Facebook

Yadda Sarkin ya gaji sarautar Zurmi

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa rasuwar ta sa ta zo ne bayan shafe shekaru biyar yana kan karagar mulkin masarautar.

Ya gaji kawunsa, Abubakar Atiku, wanda gwamnatin jihar ta tsige daga sarauta a shekarar 2021, sannan aka cire shi a hukumance a watan Afirilu na 2022.

Gwamnatin Zamfara ta cire stohon Sarkin Zurmi tare da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, bisa zargin alaka da ’yan bindiga da kuma katsalandan ga kokarin jami’an tsaro.

Daga bisani, Sarki Atiku ya rasu a wani asibiti da ke kasar Masar. Bayan haka aka nada marigayi Bello Suleiman.

Yadda ’Yan bindiga suka mamaye Zurmi

A watan Mayun 2024, ’yan bindiga sun mamaye garin Zurmi, inda suka wawashe fadar Sarki tare da kashe jami’an tsaro uku da ke bakin kofar fadar.

Maharatan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna garin, ciki har da babban jami’in tsaron Sarkin (Shamaki), Buhari Yusuf, tare da wasu mutane biyu, Aliyu Ahmed da Sa’idu Lawali.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware gwamna 1 ta ba shi lambar yabo saboda kokarin tallafawa mata

A yayin harin, maharan sun lalata wani wurin sadarwa na kamfanin MTN da ke yankin domin katse hanyoyin sadarwa tare da hana jami’an tsaro samun karin dauki.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi yunkurin sace Sarkin Zurmi

Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi niyyar yin garkuwa da marigayi Sarkin Zurmi, Bello Suleiman.

Mazauna garin sun ce maharan sun zargi marigayi Sarkin da nuna halin ko-in-kula kan zargin gallazawa da ’yan sa-kai na yankin ke yi wa Fulani mazauna garin.

Zurmi, wadda ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar tare da raba iyaka da jihar Katsina, ita ce gari na biyu mafi yawan al’umma a jihar Zamfara bayan Gusau.

Hakimin Bolari da ke Gombe ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Hakimin Bolari, Alhaji Ahmad Abubakar, rasuwa cikin daren Juma'a 28 ga watan Agustan shekarar 2026.

Rasuwar marigayin ta jefa al’ummar Bolari da sauran jama’ar Jihar Gombe cikin babban alhini da jimami, yayin da ake ci gaba da bayyana ta’aziyya da addu’o’i.

Mutane da dama sun bayyana alhininsu kan rasuwar Sarkin, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262