Gwamna Zulum Ya Kori Dagatai da Masu Unguwanni a Borno Saboda Wani Dalili

Gwamna Zulum Ya Kori Dagatai da Masu Unguwanni a Borno Saboda Wani Dalili

  • Gwamna Babagana Zulum ya kori dagatai da masu unguwanni a Malam Fatori saboda rashin kasancewa a cikin al’ummar da suke jagoranta
  • Ya umurci a fara naɗa sababbin shugabannin gargajiya masu ƙwarewa da amana wadanda za su jagoranci al'umma
  • Zulum ya bada umarnin gina makarantu da asibiti domin taimaka wa waɗanda suka dawo garin bayan shekaru na rikici

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Malam Fatori, Borno - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin dakatarwa da korar dukkan dagatai da masu unguwanni.

Gwamna Zulum ya bayar da umarnin korar ne kan dagatai da masu unguwanni na Malam Fatori, hedkwatar Ƙaramar Hukumar Abadam.

Zulum ya kori dagatai a Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Zulum ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 yayin ziyarar aiki da ya kai garin da ke kan iyakar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana ayyukan 'Hisbah' a jiharsa, ya ba jami'an tsaro umarni

Gwamnan ya bayyana rashin kasancewar shugabannin gargajiyar a cikin al’ummarsu a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, musamman a lokacin da mutanen da suka rasa matsugunansu ke komawa garin domin sake gina rayuwarsu.

Me ya sa Zulum ya kori shugabannin gargajiya?

Zulum ya ce shugabannin gargajiya suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’ummomin da suka fito daga rikici.

Ya bayyana cewa kasancewarsu a cikin al’umma na taimakawa wajen tabbatar da sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a, tare da jagorantar waɗanda suka dawo garinsu wajen sake farfaɗo da rayuwarsu.

Gwamnan ya kuma umurci Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Hon. Sugun Mai Mele, da ya haɗa kai da Shehun Borno domin fara aikin naɗa sababbin shugabannin gargajiya nan take.

Ya jaddada cewa waɗanda za a naɗa dole ne su kasance masu ƙwarewa, amana da mutunci, sannan su kasance masu iya aiki kafada da kafada da gwamnati da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Zulum zai sake gina Malam Fatori

A wani ɓangare na ziyarar, gwamnan ya yi alkawarin gaggauta sake gina muhimman ababen more rayuwa a Malam Fatori, wanda ya yi fama da mummunar barnar rikici.

Zulum ya ce shirin sake gina yankin zai taimaka wa mazauna da ke komawa garin da aka kwato daga hannun ’yan ta’adda su sake gina gidajensu da farfaɗo da sana’o’insu.

Gwamnan, tare da manyan jami’an gwamnati da ’yan majalisa, ciki har da Babban Bulaliyan Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Tahir Monguno, ya duba makarantu, gine-ginen gwamnati da gidaje da suka lalace sakamakon shekaru na rikici.

An umarci gina makarantu da asibiti

Domin dawo da rayuwa yadda ya kamata a Malam Fatori, Zulum ya bayar da umarnin gina makarantar firamare, makarantar sakandare, makarantar Islamiyya da asibitin ƙaramar hukuma.

Ya ce samar da waɗannan muhimman abubuwan more rayuwa zai taimaka wajen bai wa waɗanda suka dawo damar sake gina rayuwarsu, dawo da sana’o’insu da kuma samar wa ’ya’yansu kyakkyawar makoma.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya kafa sashen kula da kiristoci, an ji dalili

Zulum ya yi kora a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zulum ya gwangwaje mahaddata Alkur'ani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da kyautar kudi ga mahaddata Alkur'ani.

Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bai wa ɗalibai 30 da suka kammala haddar Alƙur’ani mai girma kyautar Naira miliyan 1 kowanne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng