'Za a Yi Babban Haɗari idan Tinubu Ya Bari aka Yi Faretin 1 ga Oktoba,' Ayodele
- Primate Babatunde Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan gudanar da faretin bikin ranar ’yancin kan Najeriya da za a yi ranar 1 ga Oktoba
- Ayodele ya yi ikirarin cewa akwai yiwuwar samun haɗari idan aka gudanar da faretin, tare da kira ga Shugaban Ƙasa da ya soke shi
- Faston ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da kada su karɓi wani abu daga ’yan siyasa domin samun goyon bayansu a zaɓen da za a gudanar a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Primate Babatunde Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya soke faretin bikin ranar ’yancin kan Najeriya da aka shirya gudanarwa ranar 1 ga Oktoba, yana mai cewa yin hakan na iya jawo haɗari.
Hakan na zuwa ne yayin da shugaban kasar ya cigaba da kasancewa a kasar Faransa, inda ya ke wani hutu da ya dauka.

Source: Facebook
Ayodele ya bayyana gargadin ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinsa na X yayin da ake tunkarar bikin ranar ’yancin kan Najeriya.
A bayanin da ya yi, faston ya ce idan Shugaba Tinubu ya ci gaba da shirin gudanar da faretin, akwai yiwuwar samun haɗari.
Sai dai Ayodele bai bayyana takamaiman irin haɗarin da yake magana a kai ba a bayanin da ya yi.
Kira game da zaben 2027
Malamin addinin ya kuma gargadi ’yan Najeriya da kada su karɓi wani abu daga ’yan siyasa domin musayar goyon baya a zaɓen 2027.
Daily Post ta rahoto ya ce ya kamata masu zaɓe su yi amfani da basirarsu wajen zaɓar mutanen da suke ganin za su yi aiki domin amfanin jama’a.
Ayodele ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da addu’a tare da kasancewa cikin taka-tsantsan.

Source: Facebook
An taba soke faretin 2025
A bara, Gwamnatin Tarayya ta soke faretin bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kan Najeriya da aka shirya gudanarwa ranar 1 ga Oktoba, 2025.
Gwamnatin ta bayyana soke faretin ne a wata sanarwa da Segun Imohiosen, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya sanya wa hannu.
Punch ta wallafa cewa gwamnatin ta ce soke faretin ba yana nufin an rage muhimmancin bikin ba, inda ta tabbatar da cewa sauran shirye-shiryen bikin sun cigaba kamar yadda aka tsara.
Ga bayanan da faston ya yi a bidiyo a kasa:
Tinubu yana lafiya lau
A wani labarin, mun ruwaito cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da aikinsa yayin da yake hutun aiki a ƙasashen waje.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ba sai ya kasance a Abuja ba kafin ya gudanar da ayyukansa a wannan zamani na fasahar sadarwa.
Onanuga ya kuma ce Tinubu ya ci gaba da gudanar da taruka da masu zuba jari a Faransa, ciki har da ayyukan da suka shafi shirin gina tashar jiragen ruwa mai zurfi ta dala biliyan 7 a Ogun Waterside.
Asali: Legit.ng

