Matar Aure Ta Kashe Kishiyarta a Yanayi Mara Dadin Ji, An Gano Cutar da ke Damunta
- Ana zargin wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, da kashe kishiyarta da tabarya a Tafawa Balewa Housing Estate da ke Bauchi
- ‘Yan sandan Bauchi sun ce an kama wadda ake zargin tare da kwato tabaryan da ake zargin ta yi amfani da ita wajen aikata laifin
- Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da wadda ake zargi a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Ana zargin matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, ta kashe kishiyarta, Jamila Adamu, mai shekaru 43, da tabarya a unguwar Tafawa Balewa Housing Estate da ke birnin Bauchi.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun bi dare, sun kama tare da kashe sakataren harkokin lafiya a Katsina
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana kama matar ake zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Bauchi.

Source: Twitter
A rahoton Daily Trust, Habib ya ce a ranar 27 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 4:05 na yamma, ‘yan sanda na C-Division da ke Bauchi sun samu sahihin bayani kan wani rikicin cikin gida da ya shafi wasu kishiyoyi biyu da ke zaune a gida ɗaya.
Yadda mata ta kashe uwargida
Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa amarya, Hauwa’u Haruna, tana fama da cutar da aka bayyana da sunan hallucination, wato ganin ko jin abubuwan da ba su da tushe.
An ce wannna cuta ce ta jawo ta ɗauki tabarya ta bugi uwargida, Jamila Adamu, mai shekaru 43, a goshinta, lamarin da ya sa ta faɗi a sume.
Ya ce jami’an bincike sun garzaya wurin da lamarin ya faru nan take, inda suka rubuta bayanan abin da ya faru, yayin da aka garzaya da wadda abin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi.
A cewarsa, likita ya tabbatar da cewa Jamila ta rasu, sannan aka ajiye gawarta a dakin ajiye gawa na asibitin domin gudanar da binciken gawa.
An kama matar da ake zargi
A halin yanzu, an kama wadda ake zargin, yayin da aka dauko tabaryan da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin a matsayin hujja.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin mayar da lamarin Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jiha (SCID) domin gudanar da bincike na musamman tare da gurfanar da wadda ake zargin.

Source: Original
Kwamishinan ya jajanta wa iyalan marigayiya tare da gargadin jama’a kan illar tashin hankalin cikin gida, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Ya kuma shawarci iyalai da su nemi taimakon likita da na zamantakewa cikin gaggawa ga ‘yan uwansu da ke fuskantar matsalolin lafiyar kwakwalwa.
An kama matar aure a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ’yan sandan Abuja ta kama matar aure, Rukayat Muhammed kan zargin hannu a mutuwar wani mutumi a otal a Gwarimpa.
Masu bincike sun gano cewa wayar mamacin ta ɓace, lamarin da ya sa suka fara ƙoƙarin bin diddigin wayar da kuma gano mutanen da ya yi magana da su na ƙarshe.
Sun gano mutumin da mamacin ya yi magana da shi na ƙarshe, lamarin da ya kai su ga cafke Rukayat Muhammed da ke Garki Area 2.
Asali: Legit.ng

