Kotu Ta Yi Hukunci da AA Rano da Wasu ‘Yan Kasuwa Suka Bukaci Shigo da Mai
- Babban Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta umarci NMDPRA da ta ci gaba da kyale ‘yan kasuwa su kawo mai
- Alkali ya ce ba kamfanonin AA Rano, Matrix Energy, da AYM Shafa lasisin shigo da mai bai ci karo da doka ba
- ‘Yan kasuwan sun narka fiye da dala biliyan 20 amma ana kokarin hana su kasuwanci saboda kare matatun gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a birnin Abuja ta yi umarni a bada damar cigaba da shigo da mai daga kasashen waje.
Hukuncin da aka yanke ya umarci NMDPRA ya cigaba da ba kamfanonin Matrix Energy, AA Rano da kuma AYM Shafa lasisi.

Source: Getty Images
'A bari a shigo da mai' in ji kotu
Tashar Channels ta rahoto cewa alkali ya bukaci hukumar NMDPRA ta kyale ‘yan kasuwan su sayo mai daga ketare su saida a nan.
A ranar Litinin Inyang Ekwo ya yanke wannan hukunci, yake cewa kin yin hakan yana nufin hukumar NMDPRA ta saba dokar PIA.
Raji Ahmed, SAN da Chris Ekemezie, Esq suna cikin lauyoyin da suka tsaya wa wadannan kamfanoni a kotun tarayyan na Abuja.
Lauyoyin 'yan kasuwa sun doke NMDPRA a kotu
Lauyoyin sun yi kara a kotu suna cewa babu inda dokar PIA ta 2021 ta haramta bada lasisin shigo da mai daga waje domin kasuwanci.
Raji Ahmed, SAN da Chris Ekemezie, Esq suka ce dokar PIA ba ta hana bada lasisi ba, sannan ba ta haramta tsawaita wa’adin shi ba.
Da yake yanke hukunci, Inyang Ekwo ya ce an kawo kara ne saboda ikirarin NMDPRA ta ki tsawaita tsoho ko bada sabon lasisi saboda PIA.
Alkalin ya rushe matakin da hukumar tarayyar ta dauka wanda ya ce ya ci karo da doka.
Tribune ta rahoto Mai shari’a Ekwo yana cewa masu kara sun yi nasarar gamsar da shi da hujjoji kuma lauyoyinsu sun yi galaba a karar.
'Yan kasuwar mai na neman su yi asara
Sabiu Saidu Mahuta wanda shugaba ne a kamfanin man A.A. Rano ya ce tun 2025 sai yadda NMDPRA ta ga dama ta ke ba su lasisi.
‘Yan kasuwar sun yi ikirarin sun narka $20,000,000,000 domin kasuwancin mai amma gwamnatin Najeriya tana kokarin kawo masu cikas.
Domin tsaya wa masu kara, Raji Ahmed, SAN ya ce samun lasisi a shigo da mai zai sa kamfanonin su rika gogayya da matatun cikin gida.
Bayan haka kuma zai hana a kyale wasu tsirarru su yi ta cin karensu babu babbaka a kasuwa.

Source: Getty Images
Rigimar Dangote da tsohon shugaban NMDPRA
Ana da labari cewa kwanaki Aliko Dangote ya kai karar tsohon shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, gaban hukumar EFCC a Najeriya.
Babban mai kudin da bai da sa'a a Afrika yana zarginsa da amfani da mukami ba bisa ka'ida ba da kuma cin hanci da rashawa a ofis.
Wannan ya biyo bayan janye korafin da Dangote ya yi a baya gaban hukumar ICPC, har aka yi tunanin maganar ta zo karshe kenan.
Asali: Legit.ng

