INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikatan da Za Su Yi Aikin Zaben 2027? Bayanai Sun Fito
- Hukumar zabe ta Najeriya, INEC ta musanta rahotanni da ake yadawa cewa ta fara daukar ma'aikatan wucin gadi da za su yi aikin a zaben 2027
- Hukumar ta gargadi jama’a kan wani shafin bogi da ke neman bayanan sirri da kudade, tana mai kira da mutane su yi taka tsan-tsan
- INEC ta bukaci jama’a su rika tabbatar da sahihancin bayanai daga sahihan shafukanta na kafafen sada zumunta kafin su bude hanyoyin intanet
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa ba ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi domin zaben 2027 ba.
Hukumar ta ce an jawo hankalinta kan wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa a halin yanzu INEC na daukar ma’aikatan wucin gadi tare da horas da su gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan
Da gaske Opay zai daina aiki kuma yan Najeriya za su rasa kuɗaɗensu? Gaskiya ta fito

Source: Twitter
Da gaske INEC ta fara daukar ma'aikata?
INEC ta musanta wannan jita-jita da aka fara yadawa a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2026.
INEC ta bayyana cewa wannan bayani ba daga gare ta yake ba, kuma a halin yanzu ba ta fara daukar ma'aikatan da za su yi aiki a zaben 2027 ba.
Hukumar ta kuma ce shafin da ake yadawa ba shafin daukar ma’aikata na hukuma na INEC ba ne. Ta gargadi jama’a da kada su bude shafin, su shigar da bayanansu na sirri, su dora takardu ko su biya wani kudi ta wannan manhaja.
INEC ta ce duk sanarwar hukuma da ta shafi daukar ma’aikata da harkokin zabe ana wallafa su ne ta sahihan shafukanta na kafafen sadarwa da hukumar ta tabbatar da su.
Hukumar INEC ta gargadi yan Najeriya
Hukumar ta bukaci jama’a da su ziyarci shafinta na hukuma (inecnigeria.org) domin samun sahihan bayanai.
INEC ta ce a baya ma ta gargadi jama’a kan shafukan bogi da tallace-tallacen daukar ma’aikata na karya da ake yadawa da sunan hukumar.
Ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan sanarwar daukar ma’aikatan wucin gadi ta bogi, kada kuma su sake yada ta.

Source: Getty Images
Hukumar ta shawarci jama’a da su kasance masu neman sahihan bayanai da kuma yin taka-tsantsan, tare da tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin su bude wani shafi a intanet.
INEC ta saki sunayen yan takarar gwamna
A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a jihohin Najeriya, lamarin da ya jefa ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki cikin rudani.
’Yan takara da masu ruwa da tsaki a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban a Najeriya sun shiga fargaba bayan ganin sunayen da INEC ta fitar musamman yadda aka canza wasu.
A jihar Adamawa , an sauya sunayen wadanda tun farko aka bayyana a matsayin ’yan takarar ADC, Ambasada Omar Suleiman, wanda aka fi sani da Omarana, da na PDP, Caleb Andrew.
Asali: Legit.ng
