Peter Obi Ya ba 'Yan Najeriya Shawara da Ya Sanya Kansa cikin Wadanda Suka Jefa Kasar a Matsala

Peter Obi Ya ba 'Yan Najeriya Shawara da Ya Sanya Kansa cikin Wadanda Suka Jefa Kasar a Matsala

  • Peter Obi ya ce babu wata matsala ta asali da ke damun Najeriya, sai dai rashin ingantaccen shugabanci da halayen ’yan siyasa
  • Tsohon gwamnan Anambra ya nemi addu’ar jama’a domin Allah Ya taɓa zukatan ’yan siyasa su yi amfani da dukiyar ƙasa don amfanin jama’a
  • Obi ya ce idan aka zuba dukiyar Najeriya yadda ya kamata, za a iya rage yawan matsalolin da ’yan ƙasa ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na National Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana wadanda suka haddasa matsaloli a Najeriya.

Peter Obi ya ce ’yan siyasa da rashin shugabanci nagari ne ke haddasa manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Peter Obi ya shawarci 'yan Najeriya
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Obi ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da yake jawabi a wajen taron Koinonia Global na Fasto Joshua Selman.

Kara karanta wannan

Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce babu wata matsala ta musamman da ke tattare da Najeriya, yana mai cewa babban abin da ke damun ƙasar shi ne rashin ingancin shugabancin da take samu.

“Mu ’yan siyasa ne matsalar ƙasar”

Obi ya roƙi mahalarta taron da su riƙa tunawa da ’yan siyasa a cikin addu’o’insu, domin su samu ikon yin abin da ya dace da dukiyar jama’a.

“Na yi amanna cewa mutane irinku ne ke riƙe da ƙasar nan. Abin da zan iya roƙon dukanku da kuka taru a nan shi ne ku tuna da mu ’yan siyasa a cikin addu’o’inku.”

Ya ƙara da cewa:

“Mu ne matsalar ƙasar. Babu abin da ya samu Najeriya. Abin da ke damun Najeriya shi ne shugabanci, ’yan siyasar da Allah Ya halitta a wannan ƙasa.”

Ya nemi a daina satar dukiyar ƙasa

Obi ya yi kira ga Allah Ya sauya zukatan shugabannin siyasa, domin su yi amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen inganta rayuwar jama’a maimakon amfanar da kansu.

Kara karanta wannan

'Akwai gagarumar matsala': Malamin addini ya bukaci Tinubu ya hakura da takara

Ya ce kamata ya yi shugabanni su yi amfani da dukiyar ƙasa wajen rage talauci da magance matsalolin da ke addabar al’umma.

“Allah Ya taɓa zukatanmu mu yi amfani da kuɗin jama’a don amfanin jama’a. Allah Ya taɓa zukatanmu mu daina sata. Wannan ne ya sa mutane ke shan wahala a nan.”

“Dukiyar Najeriya za ta iya sauya rayuwar jama’a”

Obi ya ce Najeriya na da isasshiyar dukiya da za ta iya taimakawa wajen inganta rayuwar ’yan ƙasa idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata, cewar rahoton jaridar TheCable.

Ya ce zuba dukiyar ƙasar cikin ayyukan ci gaba zai taimaka wajen magance matsaloli da dama da ake fuskanta.

Obi, wanda ya ce ya ziyarci ƙasashe da dama kuma ya ga yadda tsare-tsare ke aiki a can, ya danganta bambancin ci gaban ƙasashe da ingancin shugabanci.

“Na je ƙasashe da dama a duniya, kuma na ga abubuwa suna aiki a wasu ƙasashe. Shugabanci ne.” In ji shi.
Peter Obi ya ce 'yan siyasa ne matsalar Najeriya
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya nemi addu’a ga dukkan ’yan siyasa

Dan takarar ya kuma shawarci ’yan Najeriya da kada su rarraba addu’o’insu bisa la’akari da jam’iyya ko ra’ayin siyasa.

Kara karanta wannan

An gano abin da 'yan Najeriya za su yi da zai iya sa Tinubu faduwa a zaben 2027

Ya nemi su yi wa dukkan shugabannin siyasa addu’a, yana mai cewa har yanzu akwai damar magance matsalolin ƙasar.

“Kada ku ce wannan mutumin nagari ne, wancan kuma mugu ne. Ku tuna da mu duka a cikin addu’o’inku, domin za a iya magance matsalar ƙasar. Na tabbatar muku da hakan.” In ji shi.

Peter Obi ya kalubalanci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi, ya kalubalanci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya fito gaban ‘yan Najeriya kai tsaye.

Peter Obi ya bukaci Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, da kada ya dogara da wakilai ko ‘yan siyasa wajen neman ƙuri’un jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng