2027: An Yi Tururuwan Turo Motocin Tallata Tinubu Jihohin Arewa

2027: An Yi Tururuwan Turo Motocin Tallata Tinubu Jihohin Arewa

  • An kai motocin kungiyar P-BAT Door-to-Door zuwa Lafia, babban birnin Nasarawa, domin rabawa gabanin fara amfani da su wajen ayyukan gangamin siyasa
  • Wannan ya zo ne bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana wasu motoci 50 da aka bayar domin tallafa wa ayyukan APC a kananan hukumomin jihar
  • Kungiyar P-BAT Door-to-Door Movement ta ce motocin za su taimaka wajen gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da tattara magoya baya a matakin kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Motocin kungiyar P-BAT Door-to-Door Movement, wadda ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da tattara magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sun isa Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, gabanin rabasu.

An sanar da isowar motocin Lafia ne ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026, yayin da ake shirin rabasu a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sultan ya kausasa harshe kan zubar da jini, ya yi kira ga Tinubu

Motocin tallata shugaba Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallata Bola Tinubu a Lafia. Hoto: Gov Abdullahi Sule
Source: Facebook

Hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa bayanai game a isar motocin jihar Kano a wani sako da ya wallafa a Facebook.

An bayyana P-BAT Door-to-Door Movement a matsayin wata kungiya mai tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a tun daga matakin kasa.

Motocin za su kasance wani bangare na ayyukan kungiyar na tunkarar al’umma da gudanar da harkokin tattara magoya baya a jihar Nasarawa.

An kaddamar da motoci 50 a Kano

A Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana motoci 50 da Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar domin tallafa wa ayyukan APC a jihar.

Gwamnan ya ce za a raba motocin ga kananan hukumomi 44 na jihar domin saukaka ayyukan gangamin jam’iyyar da hulɗa da al’umma a matakin karkara.

Yusuf ya ce sufuri na da muhimmanci wajen gudanar da ingantaccen gangamin siyasa, domin zai bai wa jami’an jam’iyyar damar isa ga al’ummomi a sassa daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan

Dama ga matasa: Za a ɗauki 'yan soshiyal midiya 4000 domin tallata Bola Tinubu

Wakilin Tompolo, Chief Pondi Kestin, ya ce an kafa kungiyar ne domin wayar da kan jama’a kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Tarayya.

Motocin tallata shugaba Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallata shugaba Bola Tinubu. Hoto: Governor Abdullahi Sule
Source: Facebook

Gwamna Abdullahi Sule ya wallafa a Facebook cewa motocin sun isa birnin lafiya kuma za a yi aiki da su wajen tallata shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta kara kaimi

A baya-bayan nan, P-BAT Door-to-Door Movement ta gudanar da taruka da ayyukan wayar da kan jama’a a wasu jihohin Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

A Bayelsa, shugabannin kungiyar sun ce manufarsu ita ce kai bayanai game da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya kai tsaye zuwa al’umma, unguwanni da rumfunan zaɓe.

Bola Tinubu zai ciwo bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sababbin rance uku da jimillar darajarsu ta kai dala biliyan 1.5.

An tsara kowanne daga cikin rancen da darajar dala miliyan 500, inda ake sa ran za a yi amfani da kudin wajen shirye-shiryen jure sauyin yanayi, inganta ci gaban yara da kuma tallafa wa tsarin kariyar al’umma.

Bankin Duniya ya sanya 29 ga Oktoba, 2026 a matsayin ranar da kwamitinsa zai duba karin tallafin dala miliyan 500 ga shirin ACReSAL.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng