Damuna na nan Daram: NiMet Ta Jero Jihohin da za a Zagba Ruwa a Najeriya

Damuna na nan Daram: NiMet Ta Jero Jihohin da za a Zagba Ruwa a Najeriya

  • Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun hadari, tsawa da ruwan sama matsakaici a sassa daban-daban na ƙasar
  • Hukumar ta ce yanayin zai fara daga Litinin zuwa Laraba, inda wasu yankunan Arewa, Arewa ta Tsakiya da Kudancin Najeriya za su samu ruwan sama
  • NiMet ta kuma gargadi jama’a kan yiwuwar iska mai ƙarfi gabanin tsawa, tare da ba da shawarwari kan yadda za a kare kai daga illolin ruwan sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun gajimare, tsawa da ruwan sama matsakaici a sassan ƙasar daga Litinin zuwa Laraba.

A hasashen yanayin da hukumar ta fitar a Abuja ranar Lahadi, NiMet ta ce za a samu tarin gajimare a wasu sassan Arewa a safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya alfarma a 2027, ya fadi dalilin neman tazarce

Wajen da ake ruwan sama a Nafada
Yara na wasa a ruwan sama a Nafada a jihar Gombe. Hoto: Muhammad El-Nafaty
Source: Facebook

A sakon da hukumar ta wallafa a X, ta ce daga baya za a samu tsawa da ruwan sama matsakaici a mafi yawan sassan yankin.

Jihohin da za a yi ruwa

Hukumar NiMet ta ce a safiyar Litinin, za a samu yanayi mai cike da gajimare a yankin Arewa ta Tsakiya.

Hukumar ta yi hasashen tsawa da ruwan sama matsakaici a wasu sassan Abuja, Nasarawa, Benue, Kogi, Niger da Plateau daga baya a ranar.

A yankin Arewa, NiMet ta ce za a samu tsawa da ruwan sama matsakaici a mafi yawan wurare daga baya a ranar Litinin.

A ranar Talata, hukumar ta ce za a samu gajimare a wasu sassan Arewa, yayin da za a samu tsawa da ruwan sama mai sauƙi da safe a wasu sassan Borno, Gombe, Bauchi, Yobe, Taraba, Jigawa, Zamfara da Adamawa

Daga baya a ranar, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama matsakaici a mafi yawan sassan yankin.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 61, an ceto shugaban ƙaramar hukumar da ya fada tarkon yan bindiga

Hasashen jihohin Kudu

A kudancin Najeriya, NiMet ta yi hasashen gajimare tare da yiwuwar samun ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Ebonyi, Enugu, Cross River da Akwa Ibom a ranar Litinin.

Hukumar ta ce daga baya za a samu ruwan sama matsakaici lokaci-lokaci a mafi yawan sassan yankin.

A ranar Talata kuma, ana sa ran gajimare da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.

Hasashen ranar Laraba

NiMet ta yi hasashen cewa a ranar Laraba za a samu gajimare a wasu sassan Arewa, tare da tsawa da ruwan sama matsakaici da safe a sassan Taraba, Borno, Adamawa, Bauchi da Gombe.

Daga baya a ranar, ana sa ran tsawa da ruwan sama matsakaici a mafi yawan sassan yankin.

A Arewa ta Tsakiya, hukumar ta yi hasashen gajimare da kuma yiwuwar tsawa da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Nasarawa da Plateau.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

Wani waje da ake ruwan sama
Lokacin da ake ruwan sama a Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Kiran NiMet ga jama'a

Bayan fitar da hasashen, NiMet ta yi gargadin cewa iska mai ƙarfi na iya faruwa tare da tsawa a yankunan da abin ya shafa.

Ta shawarci jama’a da su ɗaure ko adana abubuwan da iska za ta iya ɗauka, domin kauce wa asarar dukiya.

Hukumar ta kuma ce kada a yi tuƙi yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi, tare da shawartar jama’a su cire na’urorin lantarki daga soket yayin tsawa.

An yi ambaliya a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa mazauna Abuja da masu abubuwan hawa sun gamu da cikas bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya.

Wuraren da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Wuse 2, Adetokunbo Ademola Crescent, yankin kusa da Delight Event Centre da ke Gudu da Efab da ke Lokogoma.

Ambaliyar ta kuma mamaye gadar da ta haɗa Gaduwa da Durumi, inda ta bar wasu masu abubuwan hawa makale tare da kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin yankunan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng