Tinubu Ya Barke da Murna bayan Najeriya Ta Samu Wani Cigaba
- Shugaba Bola Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa bayan sababbin alkaluman GDP da NBS ta fitar
- NBS ta bayyana cewa GDP na Najeriya ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 4.23 da aka samu a daidai wannan lokaci na 2025
- Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako, yana mai cewa matakin gaba shi ne tabbatar da cigaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan “hanyar da ba za a iya juyar da ita ba” zuwa samun ci gaba mai ƙarfi, bayan sababbin alkaluman GDP da NBS ta fitar.
NBS ta sanar a ranar Litinin cewa GDP na Najeriya ya samu ci gaban kashi 4.43 cikin 100 a 2026, daga kashi 4.23 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin na 2025.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a X, Tinubu ya ce alkaluman sun nuna cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar suna haifar da sakamako.
Tinubu ya ce an daidaita tattali
Tinubu ya ce bayan shekaru uku ana aiwatar da abin da ya kira sauye-sauyen da suka zama dole, gwamnatin tarayya ta samu damar daidaita tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce yanzu gwamnati za ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ci gaban tattalin arzikin ya koma ingantacciyar rayuwa ga ’yan Najeriya.
“A cikin shekaru uku da suka gabata, mun yi aikin da ya fi wahala ta hanyar aiwatar da sauye-sauyen da suka zama dole domin daidaita tattalin arziki. Yanzu tattalin arzikin ya daidaita, kuma mun kafa tubalin ƙasa mai wadata,”
In ji shi.
Tinubu ya ƙara da cewa sakamakon matakan da aka ɗauka yana ƙara bayyana, yana mai cewa Ajandar Renewed Hope tana aiki.
Shugaban ya ce sauye-sauyen gwamnatin tasa sun taimaka wajen ƙarfafa kudin asusun ƙasashen waje, da sauran wasu muhimman abubuwa.

Source: Facebook
Gwamnati za ta rage wahala
Tinubu ya ce nan da makonni masu zuwa gwamnati za ta gabatar da wasu matakai domin rage matsin tattalin arziki da ke addabar ’yan Najeriya masu rauni.
Vanguard ta wallafa cewa ya ce matakan za su haɗa da samar da sufuri mai rahusa, ƙara yawan samar da abinci da sauran shirye-shiryen tallafa wa jama’a.
Peter Obi ya soki Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya tambayi dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ke ƙoƙarin hana wata kotun ƙasar waje samun bayanan da suka shafe shi.
Obi ya bayyana damuwarsa ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, inda ya yi magana kan rahotannin matakin shari’ar da kuma batutuwan da suka shafi bayanan karatun shugaban ƙasa.
Ya ce shugaban ƙasa mai ci ya kamata ya kasance da ƙarfin gwiwar fuskantar tambayoyi kan abubuwan da suka shafi tarihinsa, maimakon hana a gudanar da bincike na halal kan irin waɗannan bayanai.
Asali: Legit.ng

