Latest
A ranar Asabar 9 ga watan Maris ne Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta gudanar da zabukkan gwamnoni da 'yan majalisun jiha a wasu jihohin kasar. An gudanar da zaben cikin lumana a mafi yawancin johohi duk da cewa akwai wasu jihohin d
Kwamanda Biu yace sun samu labarin motar tana dauke da shinkafa ne, amma an lullube buhunan shinkafar da gawayi da abincin dabbobi, haka zalika yace sun samu nasarar cafke direban motar yayin da yayi kokarin tserewa.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito uwargida Rafiat ta bayyana haka ne a zaman kotun na ranar Laraba, 13 ga watan Maris, dayake dama tun a shekarar 2016 shugaban kotun, Cif Henry Agbaje ya kashe auren ma’auratan akan Adeleke na dukanta.
Uwargidar tsohon Shugaban kasa, Justis Fati Lami Abubakar ta caccaki tsarin ci gaban siyasar kasar sannan ta kaddamar da cewar kasar Najeriya tayi rikan da ya kamata a samu wata shugaba mace.
Sama da mata 1000 ne suka yi zanga-zanga a ranar Talata, 12 ga watan Maris a Ofishin INEC da ke Sokoto inda suka bukaci hukumar da ta bayyana Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar ba tare da bata lokaci ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto, Aminu Koji, ya bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ne su ka kaddamar da harin kwanton bauna a kan jami’an ‘yan sanda Koji ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kasha jami’an ‘yan sanda biyu a harin
Da safiyar Litinin, 13 ga watan Maris mun kawo muku rahoton cewa wani gini mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune
Tsohon gwamna kuma jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Boni Haruna ya yi aman wuta akan zaben gwamnan jihar Adamawa wacce jam’iyyarsa ta lashe. Haruna yace jam’iyyar PDP ba za ta amince da kaddamar da zaben Adamawa.
Wasu Mutane a can kasar Amurka watau USA da su fito, su ka zabi wata akuya a matsayin shugabar su. Jaridun kasashen waje su ka bada wannan labari. An nada wannan dabba ne ta jagoranci al’ummar Karkarar Vermont.
Masu zafi
Samu kari