Boni Haruna ya dau zafi kan zaben Adamawa, ya bukaci INEC ta kaddamar da PDP a matsayin mai nasara
Tsohon gwamna kuma jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Boni Haruna ya yi aman wuta akan zaben gwamnan jihar Adamawa wacce jam’iyyarsa ta lashe.
Da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar PDP da ke jihar Adamawa, Boni Haruna yace jam’iyyar PDP ba za ta amince da kaddamar da zaben Adamawa a matsayin ba kammalalle ba wanda INEC tayi.
Yace hukumar zaben na ta ganawa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya saba ma tsarin dokokin da aka shimfida.
Yace kawai hukumar zaben ta kaddamar da wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris saboda dan takarar PDP ne ya lashe zaben da tazarar kuri’u masu yawa har 32,476.
KU KARANTA KUMA: Duk da taron dangi sai da Kwankwaso ya kai Gwamnatin Ganduje kasa – Sule Garo
Yace duk wani shiri na kin kaddamar da Fintiri a matsayin mai nasara a zaben zai haddasa matsala a jihar domin mutane da suka zabi dan takarar PDP a shirye suke da su kare kuri’unsu da jininsu.
Yace sake gudanar da zabe a mazabu 44 na jihar Adawa ba daidai bane da dokar zabe saboda wanda yayi nasaran na gaba ne da kuri’u 32,476.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng